Gwamnonin PDP za su shiga tsakani a rikicin jami’yyar

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad, ya ce za su haɗe kai da sauran mambobinsu wajen warware matsalolin dakatarwa da ke cikin kwamitin gudanarwa na ƙasa a jami’iyyar.

Gwamnan ya faɗi hakan ne a lokacin da tawagar ƴaƴan jam’iyyar na shiyyar Arewa-maso-Gabas ƙarƙashin jagorancin Ibrahim Damagun suka kai masa ziyara a Fadar gwamnatin jihar.

Ya ce za su bi hanyoyin da suka dace wajen ganin an dawo da martabar jami’yyar la’akari da tunkarar babban zaɓen 2027.

Gwamna Bala ya kuma yaba wa tawagar da sauran masu-ruwa-da-tsaki kan yadda su ke ba shi goyon baya, ya na mai alƙawarin zai kai jami’yyar ga ci ta hanyar haɗe kan mambobinta.

A nasa jawabin, Damagum ya ce sun ziyarci gwamnan ne don tattauna batutuwan da suka dami jami’iyyar a dukkan sassan Nijeriya tare da yaba wa gwamnan da kuma nuna goyon bayansu kan jagororin nasa.

By Babaji