Tsaro: Gwamnatin Kano ta buƙaci al’umma su ruwaito duk wani abin zargi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya kira ga al’ummar jihar su kasance masu lura da sanya ido tare da ruwaito duk wani abin zargi ga hukumomin da suka dace.

Cikin wata takarda da Mai taimaka wa mataimakin gwamnan kan harkar labarai, Ibrahim Garba Shua’ibu ya fitar, ya ce gwamnan ya kiran ne a lokacin da ya ke ƙaddamar da buɗe wani masallacin juma’a a ƙaramar hukumar Gezawa da ke jihar.

Gwamnan, wanda Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilce shi, ya ce tsaro ba abin ya da ake yi wa sako-sako ba ne don haka mutane su ke isar da saƙo ga hukumar da ta dace idan sun ga abin zargi.

Ya kuma yi kira ga dagatai musamman su riƙa sa ido kan haramtattun filaye da sayar da su da makamantansu ba bisa ƙa’ida ba a yankunansu, ya na mai cewa duk wanda bai kiyaye hakan ba, to akwai yiwuwar a soke shi daga muƙaminsa.

By Babaji