PDP ta maye gurbin ɗan takarar gwamnan Kano da Muhammad Abacha

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Jam’iyyar PDP a Jihar Kano ta tsayar da Muhammad Sani Abacha, ɗan tsohon shugaban Nijeriya Marigayi Janar Sani Abacha, a matsayin ɗan takararta na gwamnan jihar a zaɓen 2027.

Jam’iyyar PDP ta ce, ya maye gurbin tsohon ɗan takararta, Muhammad Bello Dalha, wanda ya janye daga takarar bayan tuntuɓar shugabannin jam’iyyar da sauran masu ruwa da tsaki.

Shugaban PDP na jihar, Dokta Bello Gambo Bichi, ya sanar da hakan ne a ranar Laraba yayin wani taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar a Kano.

Ya ce jam’iyyar ta gudanar da zaɓen fid-da-gwani na maye gurbin ɗan takara bayan janyewar Dalha, bisa tanadin dokokin zaɓe da kundin tsarin mulkin PDP.

Shugaban kwamitin zaɓen fid-da-gwanin, Dokta Abba Abdullahi, ya ayyana Abacha a matsayin wanda ya yi nasara, yana mai cewa an gudanar da zaɓen bisa ƙa’idojin jam’iyyar da dokokin zaɓe.

A wani ɓangare na ƙoƙarin kawo ƙarshen rikicin cikin gida, PDP ta kuma bai wa ɓangaren Kabiru Tanimu Turaki kujerar mataimakin ɗan takarar gwamna.

Daga bisani aka zaɓi Yusuf Ado Kibiya, tsohon shugaban wani tsagi na jam’iyyar kuma tsohon kwamishina, a matsayin abokin takarar Abacha.

Bichi ya ce sulhun da aka yi ya kawo ƙarshen rikicin ɓangarorin PDP a Kano, kuma yanzu jam’iyyar ta haɗe waje ɗaya gabanin babban zaɓe.

Jami’an Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) sun halarci yadda aka gudanar da tsarin.

Jam’iyyar ta kuma sauya wasu ’yan takararta na Majalisar Tarayya da Majalisar Dokokin Jihar a matsayin wani ɓangare na yarjejeniyar sulhu.

Abacha ya taɓa tsayawa takarar gwamnan Kano a zaɓen 2023, inda ya zo na uku a bayan APC, a zaɓen da jam’iyyar NNPP ta lashe.

By ukarofi

Leave a Reply