
Daga MUHAMMAD AL’AMIN a Damaturu
Babbar Jam’iyyar adawa, PDP ta sake zabar Amb. Umar El-Gash a matsayin shugabanta a zaben da ta gudanar ranar Asabar a filin wasa na 27Agust dake Damaturu, Babban Birnin jihar Yobe.
Sabon shugaban ya bayyana ķwarin-gwiwa da cewa jam’iyyar za ta samu gagarumar nasara akan abokiyar hamayyarta APC, a babban zaben 2027.
El-Gash ya ce, “A zaben da ya gabata na shugaban kasa, mun samu gagarumar nasara jihar, kuma mun shirya wajen kwace goruba a hannun kuturu a 2027, a matakin shugaban kasa da gwamnoni hadi da na yan majalisa.”
Sabon shugaban ya caccaki APC, sakamakon ci-gaba da tabarbarewar tsaro, hauhawar farashin kayayyaki, da matsalolin tattalin arziƙi a matsayin dalilan da ke sa mutane ke neman sauyi.
“Gwamnatin APC ta kasa cika alkawuran da ta daukarwa yan Nijeriya. Al’umma su na fama da mawuyacin hali—wasu ba su iya samun abinci sau biyu a rana ba. Saboda haka, yan Nijeriya sun zuba ido, su na jiran lokaci don sauya mulkin APC.”
Ya kuma bayyana nasarar da jam’iyyar ta samu a zaben 2023, inda ta lashe zaben shugaban ƙasa a Yobe a karon farko, tare da samun kujeru a majalisar wakilai biyu da na jihar daya, yana mai cewa hakan ba zai yiwu ba ba tare da goyon bayan ya’yan jam’iyyar ba.
Har’ilayau wala, ya yaba wa shugaban jam’iyyar PDP na riko a mataki na Nijeriya, Amb. Umar Iliya Damagum, wanda yake kokarin hada kan jam’iyyar tare da kasancewa shugaba abin misali.
A karshe, Amb. Umar El-Gash ya yi alkawarin zai haɗa kan ƴaƴan jam’iyyar da karfafa mata, matasa, da kafa tushe mai karfi don ci-gaban PDP a jihar.
