‘
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
‘Yan Sanda sun kama waɗannan miyagun dillalan a wani gareji da ke ƙofar ƙwayar a lokacin da suke ƙoƙarin fitar da ƙwayan zuwa garin Maraɗi a jamhuriyar Nijar.
A wata takardar sanar wa ɗauke da sa hannun mai magana da yawun yan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar ya ce mutanen dukansu matasa ne kuma yan garin Katsina ne.
“Akwai Aliyu Idris da Abubakar Sa’idu yan shekara 23 da 20 yan asalin ƙofar ƙwaya,sai kuma Tajuddeen Umar da Abubakar Suleiman yan shekara 35 da 25 suma yan asalin ƙofar ƙwaya a Katsina.
DSP sadiq ya bayyana cewa yan sanda sun sami miyagun dillalan ɗauke da kwayar Exol guda 5000 da ƙwayar Tramadol guda 400 da talatin.
Bincike ya nuna cewa suna samun irin waɗannan ƙwayoyi ne daga wani mai suna Abba da ke zaune a Abuja da yanzu haka ‘yan sanda na neman sa ruwa a jallo ya ce.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya sanar da cewa da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike za a ɗauki matakin hukunta su.
Kwamishinan ‘yan sanda CP Bello Shehu ya yaba ƙwazo da ƙwarewa da jami’an sa suka nuna wajen kamo waɗannan ɓata gari.
CP Bello sai yayi kira ga al’ummar jihar su taimaka wajan bada bayanai na sirri kan maɓoyan irin wannan ɓata gari.
