An shiga ruɗani sakamakon kisan mutum takwas da shanu 40 a Filato

Spread the love

Rahotanni daga ƙaramar hukumar Riyom da ke jihar Filato sun tabbatar da kashe mutane takwas tare da shanu kusan 40 da wasu ‘yan bindiga suka yi a daren Laraba a ƙauyen Werreng da Darwat. Shaidu daga yankin sun bayyana cewa harbe-harbe ne suka farkar da su daga barci, kuma da safiya aka gano gawarwakin mutanen da dama da suka jikkata.

Shugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a jihar, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa matasan Berom sun kai farmaki da bindigogi kan shanun makiyaya a Darwat, inda suka kashe fiye da shanu 40 tare da yankan wasu daga cikinsu, sannan suka sace naman. Ya kuma sanar da kwamandan rundunar sojojin 3 da Daraktan Tsaro na jiha.

Sai dai shugaban matasan Berom, Dalyop Solomon, ya ƙaryata zargin, yana mai cewa Fulani na amfani da yaudarar kafafen yaɗa labarai don nuna kansu a matsayin waɗanda ake zalunta. Ya ce wannan dabarar ce kawai don a karkatar da hankali daga gaskiyar lamarin da ke faruwa a yankin.

A halin da ake ciki, kwamandan rundunar Operation Safe Haven, Manjo Janar Folusho Oyinlola, ya bayyana damuwarsa kan yawaitar lalata gonaki da satar shanu a Riyom, yana mai cewa irin waɗannan ayyuka suna ƙara tayar da zaune tsaye. Sai dai sanarwar da aka fitar ba ta ambaci kisan mutane takwas da shanun ba, lamarin da ke ƙara tayar da ƙura a tsakanin al’umomin yankin.

By ukarofi