Princess Opeyemi Bright, ‘yar Najeriya mai shekaru 29 kacal, ta zama magajiyar gari mafi ƙarancin shekaru a tarihin Birtaniya. An rantsar da ita a matsayin magajiyar gari ta Barking da Dagenham a ranar 16 ga Mayu, 2025, lamarin da ya kawo sabon salo a siyasar ƙasar.
An haifi Princess Bright a Birtaniya ga iyayenta ‘yan Najeriya Dr. Councillor Afolasade Bright, tsohuwar magajiyar gari ta Hackney (2006-2007), da Pastor Gbolahan Bright MBE, babban fasto a cocin RCCG. Tun tana da shekaru 22 aka zaɓe ta a matsayin kansila, inda ta kwashe shekaru 7 tana aiki tuƙuru wajen tallafa wa matasa da inganta zamantakewa da tattalin arzikin al’umma.
A yayin rantsar da ita, Princess Opeyemi ta bayyana farin cikinta da cewa, “Wannan bai wuce rahamar ubangiji ba. Ina alfahari da kasancewata ‘yar Najeriya kuma zan wakilci gadon al’aduna da kima da ƙwazo.” Ta kuma ƙarfafa matasa da su nemi hanyoyin shugabanci da hidima ga al’umma.
Zaɓen ta a matsayin magajiyar gari ya ƙara nuna yadda ‘yan Najeriya ke ƙara tasiri a sassan duniya, musamman a fannin shugabanci da siyasa. Wannan nasara nata na ci gaba da kasancewa abin kwatance ga matasa masu burin shiga siyasa da shugabanci.
