
Daga BELLO A. BABAJI
An sake samu kefewar kwale-kwale a kauyen Gbajibo na Karamar Hukumar Kaiama ta Jihar Kwara, kusan wattani bakwai da faruwar irin haka ya yi sanadin mutuwar ďaruruwan mazauna yankin a karamar hukumar.
Lamarin na yanzu ya faru ne a lokacin da wasu fasinjoji suke dawowa daga kasuwanci a Jihar Neja, inda 27 daga cikinsu suka rasa rayukansu.
Wani shaida kuma ďaya daga cikin waɗanda suka tsira a hatsarin ya ce lamarin ya auku ne kwanaki uku da suka gabata a sakamakon dakon kaya sama da kima da aka yi wa kwale-kwalen.
Ya kuma ce baya ga haka, an samu guguwa mai ƙarfi, wadda ta taimaka wajen faruwar kefewar kwale-kwalen.
Shugaban Karamar Hukumar, Abdullahi Danladi, wanda ya jagoranci tawagar gwamnati zuwa ta’aziyyar mamatan, ya bayyana cewa gwmanatin ba za ta sake lamuntar faruwar ire-iren hatsarin ba.
Sannan, ya ce akwai shirin kafa kwamitin tilasta amfani da rigunan ninkaya da haramta tafiye-tafiyen dare da aiwatar da matakan kariya a kokarinsuna kiyayerayukanda dukiyoyin matafiyan ruwa.
A nasa bangaren, Sarkin Kaiama, Alhaji Mu’azu Umar ya ce shirye-shiryen wayar da kan al’umma za su taimaka wajen tabbatar da fasinjoji da matuka kwale-kwale sun kiyaye sharuďďan yin tafiya a ruwa.
