PDP za ta gudanar da babban taronta a Oktoba – Tambuwal

Jam’iyyar PDP ta ba da sanarwar cewar za ta gudanar da babban taronta na ƙasa tsakanin ranar 30-31 ga Oktoba mai zuwa idan Allah Ya kai mu.

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal ne ya shaida wa manema labarai hakan jim kaɗan bayan kammala wani taronsu a Abuja a jiya Juma’a.

Tambuwal ya ce za su miƙa shawarwarinsu dangane da taron ga shugabancin jam’iyyar na ƙasa, tare da cewa shugabannin ne za su tsayar da inda taron zai gudana.

Kazalika, Tambuwal ya ce sun haɗa wata tawaga ta mutum takwas ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Marka, da za su shiga su fita wajen ganin dukkan shugabannin jam’iyyar da ke da shari’a a kotu an janye komai don jam’iyyar ta ci gaba.

Tambuwal ya yi amfani da wannan dama wajen roƙon ɗaukacin ‘yan jam’iyyarsu ta PDP da kowa ya maida waƙarsa kube sannan a rungumi lumana saboda a cewarsa, Nijeriya na nan na jiran PDP, tare da cewa yana da yaƙinin za su iya magance duk wata matsalarsu a cikin gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *