Gwamnatin Zamfara ta kuɓutar da ɗaliban kwalejin da aka yi garkuwa da su

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Bayanai daga jihar Zamfara sun tabbatar da an sako ɗaliban Kwalejin Nazarin Harkokin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Jihar Zamfara, bayan kimanin makonni biyu da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga kwalejin.

A cewar Gwamna Bello Matawalle, ɗaliban sun samu ‘yanci ne ranar Juma’a da taimakon wasu tubabbun ‘yan bindiga a jihar.

An kwashi ɗaliban zuwa Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau babban birnin jihar tare da rakiyar jami’an tsaro inda gwamnan jihar tare da wasu manyan jami’an gwamnati suka karɓe su a hukumance.

Idan dai ba a manta ba, a ranar 15 ga Agusta ne da misalin ƙar 11 na dare, ‘yan bindigar suka dira harabar makarantar inda suka sace mutum 20, 15 daga ciki ɗalibai, 4 ma’aikata da kuma direba 1.

Yayin harin, ‘yan bindigar sun kashe masu gadi biyu da ɗan sanda ɗaya.

Yayin da yake karɓar ɗaliban a wannan Juma’ar, Gwamna Matawalle ya ce babu wani kuɗi da aka biya a matsayin fansa kafin sako ɗaliban.

Da yake jawabi a madadin ‘yan’uwansa, ɗaya daga cikin ɗaliban mai suna Nuhu Adamu daga ƙaramar Hukumar Gummi ta jihar, ya yaba wa Gwamna Bello Mohammed Matawalle kan yadda ya kuɓutar da su ba tare da sun samu wata nakasa ba.

Daga nan, ya buƙaci gwamnatin jihar da ta ƙara himma don kuɓutar da duk mutanen da aka sace waɗanda ke hannun ‘yan bindiga a jihar.

Kawo yanzu dai gwamnan ya ba da umarni kan a rufe manyan kasuwannin jihar.

Kazalika, ya ba da umarnin rufe dukkan gidajen mai da ke gefen gari, kana ya haramta zuwa sayen fetur da galan ko jarka a gidajen mai.