Perez ya zama shugaban Real Madrid karo na 6

Daga BASHIR ISAH

An sake zaɓen Florentino Perez ba tare da hamayya ba a matsayin shugaban ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Real Madrid a karo na shida.

Perez mai shekara 74, shi ne kaɗai ya kasance wanda ya tsaya takarar neman matsayin tun bayan da aka buɗe ƙofar takara.

Ko a 2013 da 2017 Perez ya taki wannan matsayi bayan da ya yi takarar ba tare da wata hamayya ba.

A matsayinsa na zaɓaɓɓen shugaban ƙungiyar, ana sa ran dattijon ya ja ragamar ƙungiyar ya zuwa 2025.