Legas: Ɗan sanda ya rasa aikinsa bayan da aka same shi da yinƙurin hallaka budurwarsa da bindiga

Daga UMAR M. GOMBE

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kori jami’inta Sergeant Eze Aiwansoba bayan da ta kama shi da laifin yinƙurin kisa sakamakon harbin da ya yi wa budurwarsa Joy Ndubueze a baki da bindiga.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Muyiwa Adejobi, ya faɗa a wata sanarwar da ya fitar a Litinin da ta gabata cewa, baya ga korar da aka yi wa jami’in daga aiki an kuma gurfanar da shi a wata kotun majestare da ke Yaba bisa tuhumar kisa.

A cewar Adejobi, “Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kori wani Sergeant Eze Aiwansoba daga aiki sakamakon harbi da bindiga da kuma yinƙurin kisa da ya yi kan wata budurwarsa mai suna Joy Ndubueze, a ranar 8 ga Oktoban 2020, a yankin Opebi da ke Ikeja a jihar Legas.

“Bayan an tura batun ga sashen binciken manyan laifuka da tattara bayanan sirri na rundunar jihar, sai aka gano lallai tsohon jami’in ya aikata laifi.

“Bayan da bincike ya tabbatar da jami’in ya aikata laifi, hakan ya sa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Hakeem Odumosu, ya bada damar a kore shi daga aiki. Izinin korar jami’in na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai lamba PC. 458465/LS/DFA/2, mai ɗauke da kwanan wata 2 ga Fabrairu, 2021.

Daga bisani an ɗauki Eze Aiwansoba zuwa sashen SCIID don ya fuskanci hukunci. Wasiƙar da ta bada damar sauyawa Aiwansoba wuri na ɗauke da kwanan wata 3 ga Fabrairu, 2021 kuma mai lambaAR:3100/LS/SPM/Vol.2/311

Kotun Majestaren da aka kai batun gabanta a Yaba, ta kama tsohon ɗan sandan da laifin yinƙurin hallaka Joy Ndubueze, kuma har yanzu ana kan wannan shari’ar.

Kwamishin ‘Yan Sandan jihar ya lashi takobin babu wani ɗan sanda a jihar da zai aikata laifi ya tafi siddan ba tare da ya fuskanci hukunci ba muddin aka kama shi.