Daga FARFESA AHMAD MURTALA
Ci gaba daga makon jiya.
7- Waɗannan ayyuka na POS dukkansu sun halatta ta fuskoki marasa iyaka ba tare da wani dabaibayi ba. Ga kaɗan daga cikinsu:
i- Akwai abubuwa masu yawa da banki koda kuwa wanda ba na Musulunci ba ne yake yi. Kuma ba a ƙirga su a matsayin haram. Wannan sun haɗa da tura kuɗi daga wani wuri zuwa wani “transfer’. Wannan ba wani laifi akansa. Mutum kuma zai biya banki ladan aikin da ya yi masa. Abin da masu shagunan POS suke yi a matsayinsu na wakilan banki, waɗanda ya san da zamansu a wannan sana’a, bai gaza ko kuma na ce irinsa ne kwabo da kwabo da wanda bankunan suke yi. Malaman zamani kuma bakiɗaya suka ce daidai nan yana da kyau a aikin banki. Wato ba haram ba ne a biya banki kuɗin aikin transfer- (Kararu Majma’ul Fikihil Islami: 9/1/370; Al-Bunukul Islamiyya na Abdullahi Addayar sh/25; Al-Ma’amalatul Masrafiyya Wa Hukmuha Fil Islam sh/14-15; Al-Masariful Islamiyyah: Dirasah Li Adadin Minha na Rafik Yunus Al-Misri, sh/53-55; Al-Mu’amalat Al-Maliyyah Fil Fikihil Islami Asalah Wa Mu’asarah na Debian bn Muhammad:12/234-243).
ii- A zahiri ma shagon POS wani ƙaramin banki ne da yake gudanar da wasu daga ayyukan bankin da yake da rijista da su. Lokacin da mutum ya yi amfani da ATM ya ɗebo kuɗi daga injin da banki suka ajiye don ɗibar kuɗaɗe, zai ga bankin sun ɗebi wasu ’yan kuɗaɗe na hidamar da suka yi wa mutum. Bankin da mutum yake da ‘account’ suna ɗan yi masa ragi. Amma wani bankin daban suna diba fiye da yadda nasan suka diba. Don haka, shi kansa mai POS ba dalilin da zai sa ba zai karbi wani kaso na hidamarsa ba!
iii- Masu POS cikakkun wakilai ne na karbar kudin mutum daga bankinsa zuwa nasu, sannan sai su bashi daga kudinsu. Saboda “wakilce taimako ne” kamar yadda Ibnul Arabi Al-Maliki yake fada (Ahkamul Kur’ani: 3/223). Malamai sun bayyana cewa ba laifi ka sa wakili sannan ka biyashi ko kuma in ya ga dama ya yi maka wakilcin Fisabilillahi, ba tare da an biya shi komai ba. Imamu Ibnu Kudama ya na cewa: “Ya halatta a yi wakilci ko don wani abu da za a bayar ko kuma haka kurum ba tare da shi ba”-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 5/95).
A zamanin yanzu ba dole ba ne sai an tura wani ya je bankin da kafa sannan za a ce an yi wakilci. Hatta tura kudin zuwa account din mai POS a matsayin kamar an je an karbo yake, irin abin da malamai suke kira da “Karɓar abu a Ma’ana”. Tunda kudin sun shiga lalitarsa, ba laifi don ya bayar da su ta kowace irin fuska.Wato ko ya dauko wannan da ya turawa kansa ya bawa mai kudin ko kuma ya bashi wasu da yake da su. Sannan a bashi ladansa.
iɓ- Masu POS suna yin amfani da ƙwarewarsu da wani ɓangare na kuɗin da suka sa a katin wayarsu ko na data din da suka saya. Haka nan suna amfani da wutar lantarki da injin POS din kansa da suka saya da zaman da suke yi na kudi a shaguna. Bugu da kari, sun ragewa mutane wahalar bin layin ATM ko na cikin bankuna da aka saba yi. Wannan duka a bayyane yake cewa sun yi wa mutum aiki, don haka masu POS suna da cikakken haƙƙin a biya su kuɗin wahalarsa.
‘Transfer’ da kamfonin waya suka huwacewa mutane suke yi ta hanyar amfani da wasu lambobi da kowane kamfonin waya yana da irin tasa, shi ma bai gaza irin aikin da masu POS suke yi ba. Wadannan kamfanoni suna samun wani kawo daga cikin tura kudade da mutane suke yi. Duka ya halatta.
ɓ- Kowace mu’amalla tana da asali guda biyu; “Halasci” da “Inganci”. Babu wani dalili da zai haramta sana’ar POS. Sannan kuma masu yinta a halin yanzu suna gudanar da ita bisa asalin inganci. Don haka ba haram suke ci ba, ba kuma batacciyar sana’a suke gudanarwa ba.
ɓi- Ba bu wani abu na haram ko riba a cikin mu’amalla guda biyu da ake gudanarwa ta hanyar POS. Domin riba tana shiga abubuwa guda uku ne kurum, kuma ba bu wata hanya da zasu shiga wannan mu’amalla:
a- Ciniki: Ba wata cinikayya aka ƙulla tsakanin mai POS da wanda ya zo masa don ya fito masa da kuɗi ko don ya tura masa ba. Don haka riba ba zata shiga wannan ɓangaren ba.
b- Bashi: Ba wani bashi a cikin wannan mu’amalla ta POS. Domin da ya zo shagon POS cewa ya yi yana da kudi (10,000) a cikin wannan ATM din a kwashesu a tura wani account din amma a bashi kudin cash. Wannan ‘transfer’ kenan ba bashi ba ce. Don haka riba ba zata shiga ba. Kada a ɗauka don ya zo ya bawa mai POS katin ATM ɗinsa, shi kuma ya tura kuɗi zuwa nasa ‘account’ ɗin cewa bashi ya bashi. Kuɗin kuma da zai ba shi hannu-da-hannu biyan bashin ne. Wannan ba haka ba ne. Domin ‘Ana daukar komai da manufarsa’ kamar yadda wata ƙa’ida ta faɗa. An gina mu’amallar ne a kan ‘transfer’, wadda daman bankuna suna yin ta. Mai POS ya ɗebo kuɗin daga wani ‘account’ ne ya zuba a ‘account’ ɗinsa, sannan ya bayar da su ‘cash’.
Ko da za a ce banki su ma ajiya, ake cewa mutum, ya kai musu, amma kuma aka hana mu’amallar, saboda ta ginu ne a kan bashi. Wannna haka yake ta fuskar cewa su banki tun ranar da aka kafa tsarin bankunan da aka saba da su yau da gobe (Conɓentional Banks) ya ginu ne a kan bashi da ruwa. Sañnan har yanzu haka yake a rubuce akan dokokinsu. Ko da mutane suna cewa sun kai ajiyar kudade banki, shi bankin ya san ba ajiye aka kai masa ba, shi a wurinsa rance aka ba shi. Amma sabanin wañnan mu’amalla ta POS wadda tun asali tsakanin mai kudi a ATM da mai shagon POS ba wanda yake da manufa ta bashi da rance, kowannensu manufarsa ita ce za a yi transfer ta kudi kawai. Don haka suka bambanta da tsarin da mutanen suke kira “ajiya a banki”.
Wani abu mai matukar muhimmaci da ya kamata kowa ya daɗa gane shi shine, idan har mun ƙaddara cewa, alaƙar bashi da rance ce tsakanin mai POS da mai kudi a katinsa na ATM, to abin la’akarin shi ne shi mai kudin shi ne fa ya bada rance sañnan shi ne kuma din dai ya bada karin da sunan ladan aiki. Ba wai mai shagon POS ne ya mayar da kudin da aka ranta masa (in har mun dauka ma bashi aka bashi!), sannan ya kara wani abu a kai ba. Domin malamai sun fada cewa riba ita ce ‘kudin da wanda ya karbi rance zai mayar da kudin da aka bashi da wani kari’. A mas’alar POS kuwa ba shi ne ya kara ba, shi aka karawa. Wañnan yanayin kuwa ba malamin da ya kirawoshi da sunan riba!!
A yi la’akari da wañnan sosai, domin ina ganin rashin ganeshi da fayyaceshi ne, ya sa wasu suke daukar akwai riba a mu’amalar POS, wanda kuma a hakika, kamar yadda aka gani, ba bu!
c- Canji: Duk da akwai burbushin cinikayya a cikin canji, sai dai a ilimi Fikihu ana wareshi saboda karfin ma’anar da take cikinsa wadda zata iya sawa ya ci gashin-kansa. Abin nufi dai masu POS ba canji suke yi ba. Kudin mutum ne za a bashi irinsu. Sai dai a lokacin da ya bada Naira aka tura wa ɗansa ko wakilinsa a wata jiha ko wata ƙasa, zai ɗebi daidai da canji da kimar wannan kuɗi a can.
Abin da hadisai suka hana na canji kamar wanda ya shafi dinare da dinare ko azurfa da azurfa ko naira da naira ko dala da dala shi ne, misalin a sami jan gwal sosai da kuma farin gwal, wanda ba mai ja sosai ba, sai a ce za a dauki wani abu a cikin wanda ba mai ja sosai din ba. Kamar sabuwar naira da tsohuwa, sai a ce za karbi wani abu a wurin mai tsohuwa don an bashi sabuwa. Wannan shi ne haram. Amma idan ya zamo gwal ko naira din suna wani account sai aka turashi wani account din daban sannan aka bawa mutum irinsa, shi kuma ya bada ladan wani kudi don wahalar turawa da rage masa wahalar zuwa banki da aka yi, wannan ba lifi.
Shi kuwa mai POS ya bawa mutum kudinsa yadda suke, sai dai yana cewa za a bashi kudin fito da ya yi! Ba wai mutum zuwa ya yi, a misali, ya mika masa 10,000 hannu da hannu, shi ma ya mika masa 9,990 a matsayin canji ba. Ba irin wañnan aka yi ba.
Dangane da ita kuma misali naira darin ta ladan fito, mai ATM zai iya bawa mai POS ita daban, ko kuma ya yarjewa mai POS ya hada da ita a cikin transfer din da ya yi daga cikan katin, a matsayin ladan aikinsa. Masu canji kuwa cewa zai yi zan baka sababbin ‘yan naira dari-dari na 10,000 amma zaka dora mini naira dari, to a nan sai a ce an yi riba! Domin amfanin sabuwar naira dari da tsohuwa duk daya ne, ba bu dalilin karbar wani abu a nan!
A cikin Mazahabin Hambaliyya, duk da cewa sabanin Mazahabin Jumhurun Malamai ne, amma sun halatta cewa mutumin da ya sana’anta wani gwal ya zubashi a wata kama da ado na musaman a zo a sayi gwal da kudin da ya yi daidai da shi, sannan a kara wani abu a matsayin ladan sana’arsa da fusahar da ya nuna a wajen kera dankunne da sarka da wannan gwal din. Shehul Islami Ibnu Taimiyya da Ibnul Kayyim da Ibnu Mani’, duk sun tafi a kansa haka. Sheikh Al-Mardawai ya ce, ‘A kan haka fatawar malamanmu na Hambaliyya ta gudana’. Ga kuma bayanin da Ibnu Kudama ya yi.
Ya ce: “Idan mutum ya ce da gursimeti ka kera mini zobe azurfa, nauyinsa kamar dirhami daya, zan biyaka dirhami dayan. Sannan zan baka wani dirhamin a matsayin ladan aikinka, wannan ba ya cikin irin abin da aka hana sayar da dirhami daya da guda biyu. Malaman Mazahbinmu na Hambaliyya suka kara da cewa: gursimetin zai iya karbar dirhami biyun, daya a matsayin kudin zoben, dayan kuma sakamakon ladansa“-(Al-Mugni na Ibnu Kudama: 4/130-131; Al-Majmu’u na Nawawi:10/87-88; Al-Ikhtiyarat Al-Fikhiyyah na Al-Ba’ali:sh/473; Al-Fatawal Kubra na Ibnu Taimiyyah:5/391, I’lamul Muwakki’in na Ibul Kayyim: 2/159-162, Al-Furu’u na Ibnu Muflih:4/149; Al-Insaf na Ala’uddini Al-Mardawi:5/15; Azzahbu Wa Ba’adu Khasa’isihi Wa Ahkamihi na Ibnu Mani’ a Majallar Majma’ Fikhil Islami, Al-Mu’amalat Al-Maliyyah Fil Fikihil Islami Asalah Wa Mu’asarah na Debian bn Muhammad: 11/273-322).
8- Kulawa kada mutum ya fada cikin haram ko ya ci riba yana daga cikin muhimman abubuwan da Musulmi yake kokari a kowane lokaci. Sayyadina Umar ya yi bayanin yadda mas’alolin riba suke da wahalar sha’ani wajen ganesu, sannan ya ce, “Ku kauracewa riba da duk wani abu na kokwanto”. -(Sunanu Ibnu Majah, L:2276).
Duk wata mu’amalla da wani yake yi, in ya ji shi a zuciyarsa bai gamsu da ita ba, sai kurum ya kaurace mata. Wannan kuma bai hana wadanda suka gamsu da ita su ci gaba da yinta ba, matukar akwai mafita ta Shari’a a ciki. Malamai suna fada a wata Ka’ida cewa, “Abin la’akari a mu’amalla shi ne manufa da ma’anonin da suka kunsa, ba wai zahirin lafazi da ginin kalmomi ba”.
Amma sabanin masana ko malamai a kan wata mas’ala ba shi ne yake nufin an bawa mutane damar yin zabi-ka-tika ta hanyar mutum ya zaba wani ra’ayi kurum ya darje shikenan ba! Mutum yana zabar maganar da ta fi tsayawa akan dalilan ƙur’ani da Sunna ne kurum, ba wai ya bi yarima a sha kiɗa ba! Ko ya bi hanyar tsanantawa mara tushe! Imamu Sufyanu Assauri yana cewa, “Ilimi a wurinmu shine samun rangwame daga yardajjen malami. Amma matsantawa kuwa, wannan kowa zai iya yinta”.-(Jami’u Bayanil Ilimi Wa Fadlilihi na Ibnu Abdilbarri: 2/77/ 766).
Allah ya ba mu tsayawa akan neman halal da kauracewa haram bisa yadda Shari’a ta tsara. Ya ba mu ikon tsayawa a kan tsarin addininmu da bin sahun Annabinmu – Tsira da Amincin Allah su ƙara tabbata a gare shi da alayensa da sahabbansa bakiɗaya.
Farfesa Murtala shine Shugaban Sashen Nazarin Addinin Musulunci na Jami’ar Bayeri, Kano
