Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matsalar tsadar gidaje da ke addabar mazauna Babban Birnin Tarayyar Nijeriya, Abuja, da kuma wasu manyan biranen Nijeriya na ci gaba da tsananta, inda wani bincike ya nuna cewa wasu dillalan gidaje marasa ƙwarewa suna amfani da damar da ke tattare da ƙarancin gidaje domin cutar da masu neman haya.
Binciken ya nuna cewa ayyukan da ba su dace ba da wasu dillalan gidaje ke yi suna taka rawa wajen ƙara tsadar haya, tare da jefa masu neman gidaje cikin halin ƙunci. A birane kamar Legas, Fatakwal da Kano, masu neman gidaje kan gamu da ƙalubale masu yawa kafin su samu muhalli.
A cewar wasu mazauna Abuja, kasuwar gidaje ta koma tamkar wata babbar dama ta samun kuɗi ga wasu dillalai da ke yaudarar masu neman gidaje, musamman waɗanda ke cikin matsanancin buƙatar samun muhalli.
Wata mai haya mai suna Rose Akoh ta bayyana cewa abubuwan da fuskanta daga dillalan gidaje a Abuja babu daɗi ko kaɗan. Ta ce bayan ta biya kuɗin haya na gida mai ɗakuna biyu a Kubwa har Naira miliyan biyu, an kuma karɓi ƙarin Naira dubu 400 daga gare ta a matsayin kuɗin dillanci.
Ta ƙara da cewa, duk da irin wannan kuɗi da ta biya, gidan da aka ba ta yana da matsaloli da dama. Ta ce dole ta yi amfani da nata kuɗin wajen gyaran wasu sassa na gidan, ciki har da ƙofofi da kuma kicin, duk da cewa dillalan sun yi alƙawarin za su gyara matsalolin.
Rose ta ce, a lokacin damina ma bangon gidan ya cika da ruwa, lamarin da ya ƙara mata damuwa kan lafiyar gidan.
Haka ma wani ma’aurata, Grace da Rotimi, sun ce sun sha wahala matuƙa kafin su samu gidan haya bayan aurensu. Sun bayyana cewa dillalan gidaje kan karɓi kuɗin dubawa kafin su nuna gida, wanda mafi ƙarancinsa ya kai Naira dubu biyar, yayin da wani lokaci suke biyan irin wannan kuɗi sau da dama a rana.
Sun kuma ce sau da yawa dillalan kan nuna musu gidaje daban da waɗanda suka gani a hotuna ko bidiyo, abin da ke sa su rasa lokaci da kuɗi.
Wani mai haya, Isiaka Odewale, ya ce ya fuskanci wani abin kunya lokacin da yake ƙoƙarin karɓar gidan haya a Lugbe. A cewarsa, bayan ya amince zai karɓi gidan, sai ga mutane shida sun bayyana duka suna cewa su ne dillalan gidan.
Wasu na cewa suna da alaƙa kai tsaye da mai gidan, wasu kuma na cewa su ne suka taimaka wajen rage farashin hayar. A ƙarshe dai ya karɓi makullin gidan ya bar su suna ta jayayya tsakaninsu.
Yayin da yake tsokaci kan wannan matsala, wani lauyan kan dokokin gidaje, Sunday Elisha, ya bayyana cewa a dokar Nijeriya, kuɗin dillanci bai kamata ya wuce kashi 10 cikin 100 na kuɗin haya ba.
Ya ce, idan gidan da ake haya na Naira dubu 500 a shekara, to kuɗin dillanci ya kamata ya zama Naira dubu 50 ne kawai. Amma ya ce wasu dillalai na karɓar kashi 20 cikin 100 ko ma fiye da haka, abin da ya saɓa da ƙa’idojin sana’ar.
A cewarsa, matsalar ta ƙara tsananta ne saboda rashin tsauraran dokoki da za su kula da ayyukan dillalan gidaje. Ya kuma ce wasu daga cikinsu na ƙirƙirar sabbin kuɗaɗe kamar kuɗin dubawa, kuɗin kwangila, kuɗin tsaro, kuɗin hidima da sauran su.
Sakataren reshen Abuja na Cibiyar ƙwararrun Masu Bincike da Kimanta Gidaje ta Nijeriya, wato Nigerian Institution of Estate Surɓeyors and ɓaluers, Dokta Haruna Madaki, ya yi kira da a samar da tsari mai ƙarfi na kula da ayyukan dillalan gidaje.
Ya ce, waɗanda ke karɓar kuɗaɗe masu tsada ba mambobin ƙungiyar ba ne, domin ƙwararrun masu aikin suna bin ƙa’idojin sana’ar da suka kayyade kuɗin dillanci zuwa kashi 10 cikin 100 kawai.
Madaki ya kuma bayyana cewa kuɗin tsaro da ake karɓa daga mai haya ana mayar da shi idan ya bar gidan ba tare da ya lalata kayan ciki ba.
Haka kuma mataimakin shugaban ƙungiyar Dillalan Gidaje ta Nijeriya, wato Association of Estate Agents in Nigeria, a yankin Karu na Jihar Nasarawa, Isa Angulu, ya ce yawancin matsalolin da ake gani suna faruwa ne sakamakon dillalan da ba su da lasisi.
A cewarsa, irin waɗannan mutane ne ke ƙara kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, musamman a gidajen da talakawa ke nema.
Sai dai wani dillalin gida a Abuja, John Meshach, ya kare kansu da cewa tsadar hayar gidaje ba laifinsu ba ne. Ya ce wasu masu gidaje ba sa biyansu wani abu idan suka kawo masu haya, don haka suka ƙara wasu kuɗaɗe domin su samu lada kan aikinsu.
Ya kuma danganta ƙarin kuɗin da ake karɓa da matsin tattalin arzikin ƙasar, inda ya ce hauhawar farashi da wahalhalun rayuwa sun sa dole suka ƙara kuɗin hidimarsu.
Masu ruwa da tsaki dai na ganin cewa idan ba a samar da tsari mai ƙarfi da zai kula da harkar dillancin gidaje ba, matsalar tsadar haya da damfarar masu neman muhalli za ta ci gaba da ƙaruwa, musamman a manyan biranen ƙasar.
