Raɗɗa ya karɓi jiga-jigan jam’iyyun adawa da magoya bayansu 4,000 zuwa APC a Katsina

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya karɓi dubban jiga-jigan jam’iyyun adawa da magoya bayansu su 4,000 a wani gagarumin taro da aka gudanar a ranar Talata, 21 ga Janairu, 2025, inda suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Gwamna Dikko Raɗɗa ya nuna farin cikin sa da wannan ƙaruwa da jam’iyyarsa ta samu, ya kuma bayyana cewa hakan ya samo asali ne daga addu’arsa da Allah ya amsa masa a lokacin da yake neman kujerar gwamna. 

Shi ma a jawabin sa, Mataimakin Gwamna, Honorable Faruk Lawal Joɓe, ya yi bayanin irin ayyukan alherin da Gwamna Radda ya yi tun bayan rantsar da shi, waɗanda suka haɗa da ƙirƙiro jami’an tsaro na cikin gida (Cwatch), ɗaukar sabbin malamai 7,325, samar da takin zamani, tallafawa ɗalibai zuwa ƙasashen waje, da ayyukan raya ƙasa kamar tituna da asibitoci. 

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Katsina, kuma tsohon ɗan takarar Mataimakin Gwamnan Jihar, Alh. Rabi’u Gambo Bakori, ya bayyana cewa sun yanke shawarar komawa APC ne saboda ayyukan alherin da Gwamna Radda ke gudanarwa a faɗin jihar. 

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC, Alhaji Bala Abubakar Musawa, ya gabatar da waɗanda suka sauya sheƙar, waɗanda suka haɗa da tsohon ɗan takarar Shugaban ƙasa a Jam’iyyar Accord, Alhaji Isah Hamisu, tsohon Mataimakin Gwamna, Alh. Surajo Umar Damari, tsohon Shugaban PDP, Rabi’u Gambo Bakori, Shugaban ƙungiyar Dikko Project, Hon. Musa Gafai, da sauran ƙusoshin jam’iyyun NNPP, LP, da sauransu.

Taron ya samu halartar Sakataren Gwamnati, Barr. Abdullahi Garba Faskari, Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnati, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, Sakataren Gwamnan, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, da sauran manyan jami’an gwamnati.

By ukarofi