Koyar da ilimin jima’i a makarantu

Spread the love

Yanzu dai ta tabbata, ma’aikatar ilimi ta ƙasa ta bai wa hukumar kula da shirya jadawalin koyarwa a makarantu ta NERDC ta cire duk wani abu da ya shafi ɓangaren koyar da ilimin jima’i a makarantun ƙasar nan. Matakin da ƙungiyoyin sa kai na al’umma su 54 suka haɗu wajen ƙalubalantar wannan mataki na Gwamnatin Tarayya, bisa hujjar cewa hakan zai iya dawo da hannun agogo baya, a yaƙin da ake yi da yaɗuwar cutar HIV mai karya garkuwar jiki.

Masu goyon bayan wannan tsarin na ganin koyar da yara sanin ilimin jima’i zai taimaka musu wajen sanin mai ya kamata su yi a lokacin da wani babba ya afka musu da nufin fyaɗe ko masu lalata da ƙananan yara, daga cikin abokan karatu, gurɓatattun da wasu makusanta na gida ko na anguwa, musamman yadda cutar HIV mai karya garkuwar jiki take yaɗuwa, da sauran cututtuka da ake samu daga jima’i marar tsafta.

Har wa yau kuma, ana danganta matsalolin da yara mata da ke shekarun fara al’ada suke fuskanta, samun shigar cikin da ba a shirya shigarsa ba, ta dalilin fyaɗe ko yaudarar wasu maza, da kuma damuwoyin da ake samu yayin zubar da ciki ko amfani da magungunan hana ɗaukar ciki, kan rashin samun ilimin jima’i da wuri, da ba su shawarwarin da ya dace a kan lokaci.

Tun farkon shigo da wannan tsari kimanin shekaru 20 da suka gabata a makarantun Nijeriya, ya sha suka sosai a wajen malaman addini, masana tarbiyya da iyaye, waɗanda ke ganin illar yin hakan ga gyaruwar tarbiyyar ƙananan yara da ke tasowa da tunanin gwada duk wani abu da suke ji ko gani, domin tabbatar da yadda yake, ba tare da sun san illoli ko rashin dacewar hakan ba.

Lallai dole malamai da masu nazari kan harkokin ilimi su koka ga irin wannan tsari na koyarwa da bai dace da ƙananan yara da ba su balaga ba, ko kuma suke da ƙananan shekaru, domin tasirin da hakan ke da shi ga tarbiyyarsu da tunanin su. Wannan tattaunawa ba kasafai iyaye ke zama su yi shi da yara ba, saboda kunya da al’ada. Kamar yadda mahaifiyar Zainul Abideen ta kasa natsuwa ta saurari tambayoyin da ɗanta yake yi wa babansa ba. Fahimtarta tayi daidai da tawa, inda muke ganin wannan koyarwa ba ta dace da ƙananan yara irin sa ba.

Ko da yake mun taso a al’adance a nan ƙasar Hausa sai yaro ya girma har ya kusa balaga ne sannan yake fara sanin wasu abubuwan, kafin wani wansa ko malaminsa na Islamiyya ya fara koya masa abubuwan da, suka wajaba a kansa na game da ayyukan ibada da zaman aure. Haka ita ma mace daga lokacin da ta fara jinin al’ada, a lokacin ne mahaifiyarta ko ƙanwar mahaifiyar ta ke sanar da ita wasu abubuwa da ya kamata ta kula da su, da kuma a makaranta wajen karatun ilimin addini, inda malaman fiƙhu suka yi bayani dalla dalla, game da hukuncin addinin Musulunci a game da waɗannan muhimman batutuwa da suka shafi al’ada, balaga, jima’i da zamantakewar aure.

Yadda rayuwa ta canza a halin da ake ciki, abubuwa na ilimomi na nan birjik a kafafen sadarwa na zamani, wanda ba ka buƙatar zaunar da yaro ka koya masa wani abu, sai dai ƙoƙarinsa masa ido da tarbiyyar da shi a kan tsarin addini da halayen ƙwarai, don kada ya yi amfani da ilimin da yake gani a yanar gizo ta inda bai dace ba.

Wasiƙa daga AISHA ISAH. 09070905293.

By ukarofi