Daga DANLADI Z. HARUNA
Hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) ce ke da alhakin aiwatar da kiranye kamar dai yadda take gudanar da zaɓe. Kiranye shi ne dawowa daga rakiyar wakilcin zaɓaɓɓen ɗan siyasa ke yi wa al’ummarsa.Zaɓaɓɓen ɗan siyasa shi ne wanda ya yi nasara a zaɓen ƙarshe da aka gabatar a yankin da yake wakilta. Kundin tsari mulki na Nijeriya sashe na 69 da na 110, kazalika da dokar zaɓe ta 2022 sashe na 116 ne suka ƙarfafi hukumar zaɓe ta ƙasa da ta gudanar da kiranye ga ƴan wakali a jiha ko na tarayya gami fa shugabannin ƙananan hukumomin birnin tarayya Abuja.Da zarar hukumar ta INEC ta karɓi rubutacce kuma halastaccen ƙorafi daga al’ummar yankin da wakilin yake, sai ta shiga haramar aiwatar da kiranye.
Halastaccen ƙorafi:Ba kowanne ƙorafi ne halastacce ba a fuskar doka. Wajibi ne ƙorafi ya zama a rubuce. Kuma daga al’ummar yanki waɗanda suke da katin zaɓe. Sannan wajibi ne a samu kashi 50 cikin na mamallakan ƙuri’a sun saka hannu a takardar ƙorafin.Wato misali, idan yankin mazaɓar Daddarawa na da rijistar masu zaɓe dubu goma, to sai dubu biyar sun saka hannu akan ƙorafin kafin ya zama halastacce.
Miƙa ƙorafi:Idan masu ƙorafin sun shirya, suna iya tunkarar hukumar zaɓe, domin ta ba su kwafin amintattun masu riƙe da ƙuri’a, wato ‘Certified True Copy’.Da zarar an ba su kwafin, sai su soma tattara sa hannun jama’a har a samu adadin da ake so. Idan an kammala saka hannun sai a miƙa wa hukumar zaɓe, ita kuma za ta yi nazari da tantance sahihancin bayanan.Idan hukumar ta gano akwai kuskure ko kuma wata ƙa’ida da ba a cika ba, sai a jawo hankalin al’ummar domin su gyara. Idan ba su gyara ba, sai a jingine batun har sai sun cika dukkan ƙa’idojin.
Tantancewa:Idan kuma ƙa’idojin duka sun cika sai a saka ranar tantancewa, watau ‘ɓerification’.Tantancewa iri biyu ce. Irin na farko ana kiran ta ‘Recall ɓerification’, wato masu zaɓen da suka saka hannu su fito su jaddada cewar lallai su ne suka amince a yi wa wakilinsu kiranye. Wajibi su kai aƙalla kashi 50 na masu rijista a yankin ko sama da haka.Nau’i na biyu kuma ana kiran sa ‘Referendum Recall’, wato dukkan jama’ar yanki bakiɗaya su fito su kaɗa ƙuri’ar Eh ko A’a ga wakilinsu. Wajibi ne masu Eh su kai kashi 50 na masu kaɗa ƙuri’a ko fiye da haka kafin kiranyen ya tabbata.Idan adadin bai kai yadda aka ambata ba, sai hukuma ta sanar da cewa, ba a yi nasarar kiranyen ba, amma masu ƙorafi na iya sake aiwatar da wani kiranyen yadda za su yi nasara.
Tsawon lokaci:Daga ranar da hukumar zaɓe ta karɓi ƙorafi zuwa kammala komai da komai, tilas ne a ƙarƙare shi cikin kwanaki 90. Idan an haura hakan, an shiga wani abu kuma.A tsakanin wannan lokacin, masu ƙorafin na iya janyewa su ƙyale wakilin nasu ya yi ta yi.Kowanne wakili shi ɗaya za a yi wa kiranye. Ba a haɗa wani da wani. Misali, ba za a iya yin ƙorafin akan ɗan majalisar Amarawa da na ƙyaƙyatawa a ƙorafi guda ba.Haka nan ba a haɗa ƙorafi kan ɗan majalisar jiha da na tarayya a waje guda ba, ko kuma a haɗa su da na sanata ba. Kowa mazaɓarsa daban, wato ‘constituency’.Idan ranar yin zaɓen na raba gardama ta zo, kowa akwatinsa za shi ya bayyana ra’ayinsa, wato ko dai ya tabbatar da sa hannunsa ko kuma ya jefa ƙuri’ar Eh ko A’a.
Sau nawa kiranye ya yi nasara?A sani na tun daga 1999 zuwa yau, an jarraba yin kiranye kamar na George Okoye, Simon Lalong, Dino Malaye, Farouk Adamu Aliyu da Umar Jibril. Duk waɗannan yunƙuri an yi an gama ba tare da nasara ba duk da ƙarfin tuwon da gwamnoni suka nuna a yunƙurin.Don haka masu shirin yi wa wakilansu kiranye ƙofa a buɗe ta ke, amma fa ba ta ɓullewa.
Danladi Haruna marubuci ne kuma manazarci a Kano, Nijeriya
