Rahoto na musamman: Shahararrun ’yan sandan Nijeriya da suka fuskanci zargin rashawa

Daga AMINA YUSUF ALI

Wasu manyan jami’an tsaron ’yan sanda, waɗanda a baya suka yi shuhura kuma suka yi fice ta fuskar yaƙi da masu aikata laifuka da masu yi wa tattalin arziki ƙasa ta’annati, masu harkar miyagun ƙwayoyi, ta’addanci da kuma sauransu kafin su ma tasu dubun ta cika ayyukan nasu da farinjininsu  suka zube warwas kamar ba a yi su ba.

Ga wani bincike da aka gudanar a kan waɗannan jami’an tsaron ma’abota shuhra na wani lokaci.  daga ƙarshe suka yi wa ɗaukakar da suka samu a sana’arsu  ƙamshin mutuwa. 

Tsohon Sufeto Janar ɗin ‘Yan Sanda, Tafa Balogun:
Tafa Balogun tsohon Sufeto Janar na ‘Yan sanda ne wanda tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjobya naɗa shi a cikin shekara ta 2002. A lokacin ya samu hukumar tsaro a cikin halin fatara na rashin samar da walwala da horo ga jami’an. Sannan ga yawaitar laifuffuka kamar fashi da makami sun yi tashin gwauron zabi a wancan lokaci.
Balogun shi ma ya taka rawar gani a zamaninsa. Inda ya samu ya saita al’amura kuma ya samu nasarori waɗanda suka sa ya zama abin alfahari ga hukumar ‘yan sanda da kuma ga sauran al’umma. 

Bayan wasu lokuta kuma, sai salon aikin nasa ya canza, inda IG ɗin ya fara ɓoye wasu al’amuran nasa ga abokanen aikinsa kuma ya fara yi wa wasu sassa a hukumar katsalandan cikin alamuransu.

Haka ya cigaba da shan sharafinsa kafin dubunsa ta cika a watan Janairun shekara ta 2005. A lokacin da hukumar mai yaƙi da cin hancin da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, EFCC a ƙarƙashin shugabancin Nuhu Ribaɗo ta nemi ta binciki wasu ɓoyayyun laifuffuka da shi Balogun yake yi da suka saɓa doka. Wannan labari ba ƙaramin girgiza al’umma ya yi ba. Saboda haka, ba yadda ya iya, dole ya ajiye aikin ‘Yan sanda.

Bayan ajiye aikin nasa ne a watan Maris ɗin shekara ta 2005, Hukumar ta EFCC ta gurfanar da shi a Kotun Ƙoli ta Tarayyar ƙasar nan inda aka zarge shi da laifuffuka har 56 waɗanda suka haɗa da lulluɓe wasu laifuka da ya tafka don kada hukumar EFCC ta ɗago shi. Wato shigar da son zuciya don amfana daga wasu kamfanoni.

Sai bayan watanni biyu, da su]in goshi da ƙoƙarin lauyansa da roƙo da ban-baki, aka samu aka daidaita kotu ta rage laifukan suka koma guda takwas kuma kowanne daga cikinsu hukuncin watanni shida a gidan yari ko zaɓin tarar Naira dubu ɗari biyar a kan kowanne daga laifukan.
 
Kotu ta umarce shi ya biya tarar Naira miliyan huɗu, sannan aka ƙwace kadarorinsa guda 14 da suke a Lagos da Abuja, sannan aka ba da umarni ga hukumar kula da Harkokin Kamfani umarnin ta soke rajistar dukkan  kamfanoninsa. 

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Ibrahim Magu:
Mataimakin Kwamishinan ‘Yan sanda, Ibrahim Magu Ya fara samun shuhra ne saboda jajircewarsa a kan yaƙi da rashawa tun bayan naɗinsa da Shugaban ƙasa Buhari ya yi a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon-ƙasa, EFCC a shekara ta 2015. Kodayake wasu suna zargin Magu da kasancewa karen farauta ga shi shugaban domin ana amfani da shi don hana ‘yan siyasa na jam’iyyar adawa, rawar gaban hantsi.

Magu ya fara shiga tsaka mai wuya ne a shekarar 2016 lokacin da hukumar jami’an tsaro na farin kaya, DSS ta fara zarginsa da facaka da kuɗi da suka wuce misali. Kamar danƙareren gidan da yake zauna na miliyan 40, ga hawa jirgin sama na gida, sannan da uwa uba karɓar rashawa daga mutanen da hukumar EFCC take bincika.

Sannan kuma akwai tashin-tashina game da sahihancin halascin naɗin da aka yi masa na shugabancin EFCC. Inda ake tantamar ko bai ci jarrabawar da majalisar dattawa ta yi masa ba na neman cancantar zama jagoran EFCC. Inda ake zargin bai samu kaso mai yawa na goyon baya daga Sanatocin ba.
 
Bayan waccan ƙurar ta lafa kuma, a watan Yunin shekarar da ta gabata ta 2020 kuma, Babban Antoni Janar na tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya aike da wata wasiƙa ga shugaban ƙasa wacce take ƙunshe da neman a tsige Magu daga muƙaminsa domin rashin cancantarsa na cigaba da shugabantar EFCC. Bisa laifin karkatar da kuɗaɗen da aka ƙwato na rashawa zuwa buƙatunsa, da almubazzaranci da sauransu.

Daga nan shugaban ƙasa ya kafa kwamitin binciken Magun a ƙarƙashin shugabancin tsohon Mai Shari’a, Ayo Salami. Inda aka nemi Magun ya ɗan matsa daga kujerar tasa don a ji daɗin ci gaba da binciken, sai dai komawar da bai yi ba kenan, har yau.

Tsohon Kwamishinan ‘Yan Sanda, Fidelis Oyakhilome:
Fidelis Oyakhilome wani tsohon kwamishinan ‘yan sanda ne a ƙarni na 19 wanda ya sha sharafinsa a fagen aikin ɗansanda tun lokacin da ya shiga fagen a shekara ta 1959.

Oyakhilome ya taɓa riƙe muƙamin Gwamna a Jahar Ribas a zamanin mulkin soja, a jamhuriyya ta biyu.  Inda ya kawo abubuwan cigaba a jihar har da bunƙasa fannin noma. 
Fidelis Oyakhilome ya haɗu da azal ne a lokacin da yake shugabantar hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi, NDLE a shekarar 1988. A inda aka cafke shi a kan zargin karɓar cin hancin don ya sallami wasu masu laifi. Ya karɓi kuɗin ne a wajen wata ‘yar Kasuwa wacce ake zargin tsohon gwamnan da ita suna yin soyayya. Kuma ita wannan mata ana zargi dila ce a harkar sayar da kayan maye. Kuma ta taɓa shan sarƙa saboda wannan laifi nata. 

Mataimakin Kwamishinan ‘Yan Sanda, Abba Kyari:
Shi ma wannan mataimakin kwamishina mai suna Abba kyari ya fara shiga sahun shahara ne tun daga shekara ta 2017. A yayin Runduna ta musamman dake kai ɗauki ta fuskar aiki da bayanan sirri a hukumar Ƴansanda da yake shugabanta ta cafke wani ɗan ta’adda da ya yi ƙaurin suna Chukudi Onuamadike wanda aka fi sani da Evans. Shuhrar tasa ta ƙara bunƙasa har a shafukan yanar gizo yayin da rundunar tasa ta cigaba da murƙushe ‘yan Boko Haram da ɓata-gari.

Bayan wani ɗan lokaci ne kuma, ‘yan Najeriya suka soma dawowa daga rakiyar Kyari yayin da aka fara kokwanton kyawawan ɗabi’unsa  bayan da aka fara zargin cewa yana karkatar da dukiyoyin wasu mutane da ya kama i zuwa amfanin ƙashin kansa sannan kuma da alaƙarsa da mutanen da aka san cewa ba nagari ba ne. Kuma labaran sun cika ko’ina a shafukan yanar gizo. 
Farin jini da kwarjinin Kyari sun ƙarasa zubewa ne warwas bayan a ranar 26 ga watan Yulin shekarar nan, bayan da wata kotu a ƙasar Amurka ta ba da umarni ga hukumar binciken laifuka ta FBI da ta cafke shi a kan ba da gudunmowa cikin wata harƙallar damfara ta miliyoyin dalar Amurka da wannan ƙasurgumin ɗan damfarar Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi da tawagarsa suka yi.

Hushpuppi dai wani biloniyan ɗan damfara ne wanda ya yi ƙaurin wajen facaka da kuɗi wanda hukumar Daular Ƙasashen Larabawa ta damƙe  shi ta miƙa shi ga hukumar Ƙasar Amurka a kan zargin damfara da wankiya, da kutsen na’ura mai ƙwaƙwalwa, da sauransu.

Inda kotun dai ta Amurka ta kuma zargi shi ma Kyarin a kan karɓar cin hanci daga Hushpuppi domin a kama kuma a tsare masa abokin sana’ar shi Hushpuppi ɗin wato Chibuzor Vincent.

Wannan al’amari ya jawo Sufeto Janar ɗin ‘yan sandan Najeriya wato Usman Alkali Baba ya sallami shi Kyarin daga aiki a hukumar ‘yan sandan ma gabaɗaya a ranar 1 ga watan Agustan shekarar nan da muke ciki. Duk da cewa shi Kyarin ya musanta zargin da ake yi masa inda ya alaƙanta haɗakarsa da Hushpuppi da cewa shi Huspuppin ya nemi ya sayi irin wasu kaya da ya gani a jikin Kyari, shi kuma ya haɗa shi da mai sayarwar inda ya saya ya biya farashin Naira dubu ɗari uku.

A wannan gaɓar ne wani Malamin Jami’ar NOUN daga sashen fahimtar zamantakewa, Dakta Aminu Umar ya bayyana cewa, babbar matsalar da take saka wa jami’an tsaro su tsunduma harkar cin rashawa shi ne, yadda ake bin wasu alaƙoƙi na iyayen gida wajen naɗa su muƙamai. Ko ba su cancanta ba, idan suna da ubangida mai ƙarfi, sai a naɗa su. A ƙarshe garin biyayya ga iyayen gida ko matsalar kuɗi su faɗa a halan-halahu. Wanda su ma iyayen gidan sun zaɓe ka ne saboda tasu biyan buƙatar. Duk da cewarsa dai akwai waɗanda ake naɗawar bisa cancanta.

Amma shi a nasa ra’ayin wani masani akan harkar tsaro, Bem Japhet Audu. Ya bayyana cewa, dokar ƙasar nan ce matsala. Inda ya ce dokoki da yawa a ƙasar nan an yi su, kuma an bar su kara-zube, ba a amfani da su. Sannan kuma a cewarsa hukumomin tsaro an ba su ikon da ya wuce minsharrin. Don haka don sun yi cin hanci da rashawa ba abin mamaki ba ne. 
Shi kuma a nasa tunanin, tsohon Manjo mai ritaya, Manjo Bashir Galma yana ganin ba laifin hukuma ko wasu mutane ba. Illa ra’ayin ƙashin kai na kowanne jami’in  da zai iya saka shi ya zama na gari ko akasin haka.

Ya ƙara da cewa su ma shugabanni su dage su sauke nauyin mutane domin a rage faruwar cin hanci da rashawa a ƙasar nan.

Mun fassaro ne daga 21st Century Chronicle.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *