Yadda za ki iya magance matsalar sanyi da kanki

Daga BILKISU YUSUF ALI

Tambaya:
Salam Malama Bilkisu, na karanta bayaninki a satin da ya gabata kan mene ne ciwon sanyi da hanyoyin magance shi, amma sai na lura kamar mata ne ke da larurar, ban da maza. Shin haka ne?

Amsa:
Amin wa alaikassalam ba mata kaɗai ke fama da larurar sanyi ba, amma matan sun fi saurin kamuwa sannan ciwon ya fi naci a gurinsu, musamman saboda yanayin halittarsu da kuma yadda suke mu’amala da banɗaki da tufafinsu na ciki da sauransu. Amma kafin mu faɗa kan matsololin maza da ciwon sanyi bari mu kammala da yadda mace za ta magance maganin sanyi.

Shan Kanumfari da tafarnuwa da babunaj kamar shayi yana magance matsalar sanyi da ake ɗauka.
Yayin magance matsalar sanyi ga mace tana buƙatar kulawa da waɗannan sharuɗɗa:-

-A kiyaye tsaftar pant kuma in an jima ana amfani da shi ya kamata a sauya wasu ko a wanke a shanya su a rana.
-Mata su kiyaye cushe-cushe a gabansu don da dama magungunan da suke sa wa suna ɗauke da ƙwayoyin cuta wasu wurin haɗawa wasu kuma a mazubin da aka saka su wasu ma a hannayenki ba ki sani ba.
-Neman magani a inda ya dace
-Yin magani na tsawon lokaci saboda ciwon sanyi yana da naci.
-Yin maganin tare da abokin zama saboda ɗauka ake yi.
-Yin dogon zama a kan toilet yayin bayan gida.
-Lokacin yin tsarki in an yi bayan gida a fara ta gaba sannan baya.
-Kula da tsarki a tsaftace shi sosai musamman lokacin al’ada.
-Rashin barin ƙunzugu/Pad ta jima a jiki.
-Tsarki da ruwa mai sanyi sosai
-Zama a ƙasa musamman a kan tiles
-Wasa da gaba (jima’in hannu) Saboda hannu masana suna faɗa yana ɗauke da wani dafi.

In sha Allahu in dai za a kiyaye waɗannan dokokin tare da shan maganin da ya dace na sanyi za a samu waraka. A mako na gaba za mu amsa tambayar da aka turo kan matsalolin maza na sanyi da hanyoyin magance su.

Ga mai tambaya ko neman wani ƙarin bayani yana iya tuntuɓar wannan layin amma tes kawai ko ta whatsup 08039475191 ko a shafina na Facebook mai suna Bilkisu Yusuf Ali.