Ramadan 2022: A nemi jinjirin wata gobe Juma’a – NMSC

Kwamitin Neman Wata na Ƙasa (NMSC) na Majalisar Ƙoli na Harkokin Musuluncin Ƙasa (NSCIS), ya bada sanarwar al’ummar Musulmin Najeriya a nemi watan Ramadan gobe Juma’a idan Allah Ya kai mu.

Kwamitin ya ce gobe Juma’a take 1 ga Afrilun 2022 wanda ya yi daidai da 29 ga Sha’aban, 1443, wanda hakan ya zama ranar farko da ya kamata a nemi watan na Ramadan 1443.

NMSC ya bada sanarwar ta hanyar wallafawa a shafinsa na facebook.

Kwafin sanarwar

Idan Allah Ya sa aka ga wata a goben, hakan na nufin al’ummar Nijeriya za su tashi da azumi Asabar mai zuwa kenan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *