Ramadan: Ku nemi jinjirin wata gobe Laraba, kiran Sarkin Musulmi ga Musulmin Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Ƙoli Kan Harkokin Addinin Musulunci a Nijeriya (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su nemi jinjirin watan Ramadan na bana bayan faɗuwar rana a ranar Laraba.

Daraktan gudanarwa na Majalisar, Arc. Zubairu Haruna Usman-Ugwu, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ranar Litinin a Abuja.

Ya ce “sakamakon shawarar da Kwamitin Duban Wata na Majlisar ya bayar, Sarkin Musulmi ya buƙaci musulmin Nijeriya da su nemi jinjirin watan Ramadan na shekarar 1444 A.H. da zarar ranar ta faɗi ya zuwa ranar Laraba, 29 ga Sha’aban, 1444 A.H. wanda ya yi daidai da 22 ga Maris, 2023.

“Idan aka ga jinjirin watan a wannan yammaci, Sarkin Musulmi zai ayyana ranar Alhamis, 23 ga Maris, 2023 a matsayin ranar farko ga Ramadan, 1444 A.H.

“Idan kuwa ya zamana ba a ga wata ba, kenan Juma’a 24 Maris 2023 ta zama 1 ga Ramadan,” in ji Usman-Ugwu.