Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU
A cikin wannan mako mai ƙarewa ne aka gudanar da bikin Ranar Nakasassu ta Duniya ta shekarar 2024, wacce ta mayar da hankali wajen duba yadda za a shigar da masu nakasa cikin harkokin cigaban al’umma ba tare da nuna musu wariya ko ƙyama ba.
Rahoton Majalisar ɗinkin Duniya ya bayyana cewa fiye da kashi 15 cikin ɗari na al’ummar duniya suna rayuwa da wata nakasa, kashi 80 daga cikinsu suna rayuwa ne a ƙasashe masu tasowa irin Nijeriya. Waɗanda ke rayuwa cikin ƙunci da rashin samun kulawar da ta kamata, daga hukumomi ko daga jama’ar gari, musamman ma dai ’yan uwa da iyali.
A shekarar 1992 ne Babban Zauren Majalisar ɗinkin Duniya ya amince da ware ranar 3 ga watan Disamba na kowacce shekara ya zama ranar da ƙasashen duniya za su yi nazari kan rayuwar masu buƙata ta musamman da ƙalubalen da suke fuskanta, har da buƙatun su a wajen hukumomi da masu faɗa a ji. Sannan a ƙara fahimtar da jama’a buƙatar bai wa masu nakasa damar ba da gudunmawa a ɓangaren siyasa, sha’anin mulki, tattalin arziki da ilimi.
Ana amfani da kalmar nakasa ne ga mutanen da suka rasa ganinsu wato makafi, da guragu, da kutare, da kurame, zabiya da masu nakasar ƙwaƙwalwa. Har yanzu bincike na nuni da cewa ana ƙara gano sauran nau’o’i na nakasa da ba sa cikin waɗancan nau’o’in nakasa da aka fi sabawa da su, kamar mutane masu kasa koyon wani sabon abu, ko ɗaukar karatu a aji, ko masu tsoron duhu, ko waɗanda ba sa iya gane darasin lissafi a makaranta, duk ana yi musu kallon masu ɗauke da lalurar nakasa. Bincike ya nuna cewa a ƙasashen da talauci da jahilci suka fi yawa, an fi samun mutane masu nakasa, saboda rashin ƙwararrun likitocin, rashin ingantattun asibitoci da makarantu, rashin hanyoyin mota masu kyau, da kuma yadda jahilci da al’adu ke sa wasu iyaye ɗora alhakin kamuwa da wasu lalurorin kan canfe-canfe, da zargin mayu ko iskokai, kan wasu lalurorin da za a iya magance su, idan an nemi shawarar ƙwararru da wuri.
Waɗannan na daga cikin dalilan da ke sa a riƙa nuna wa masu buƙata ta musamman, ƙyama da rashin kulawa. Sannan wasu da dama daga cikinsu, musamman mata, suna fuskantar matsalar fyaɗe da cin zarafi, ko rashin samun miji da wuri da saurin mutuwar aure.
ƙudirin kare haƙƙoƙi na Majalisar ɗinkin Duniya na 9 ya buƙaci a ɗauki kowanne mutum mai nakasa a matsayin mutum mai cikakken ‘yanci, kamar kowa, kuma a tsare musu mutuncinsu da martabarsu a duk inda suka samu kansu. A kula da inganta lafiyarsu, da makarantunsu, da shigar da su cikin sha’anin tafiyar da gwamnati, domin masu ƙwarewa da ilimi a cikinsu su samu damar bayar da gudunmawarsu.
Na samu damar zantawa da wasu nakasassu da suka halarci wani taron Ranar Nakasassu ta wannan shekara da wata ƙungiya mai zaman kanta ta shirya a Jos, da nufin jawo su a jiki da taya su murna kan wannan rana ta ake tattaunawa kan muhimman batutuwan da suka shafi cigaban rayuwar su. Daga cikin bayanan da suka yi min har da batun yadda ake yi musu kallon ƙasƙanci da rashin nuna kulawa da lamarinsu hatta a ɓangaren iyali ko wurin ibada.
Wani abu da ya sosa min zuciya daga cikin hirarrakin da muka yi har da wani da ya nuna min cewa ko a masallaci idan sun shiga sahu ana samun masu nuna musu ƙyama, ba sa son su haɗa kafaɗa ko sahu ɗaya da su. Sannan hatta wajen shiga masallacin ba ko ina ne za ka shiga ka ga an yi hanyar shiga yadda mai nakasa, gurgu ko makaho zai iya bi ya shiga ba.
Na taɓa yin rubutu game da wani yaro da Allah Ya jarabce shi da lalurar shanyewar ƙafafu, sakamakon allura a asibiti, amma maimakon iyayen su mayar da hankali wajen inganta rayuwarsa da nuna masa dukkan gatan da yake buƙata, don ya taso ba tare da ya ji a ransa cewa shi ƙasasshe ba ne, sai aka riƙa tura shi bakin hanya yana bara, yana nemo wa iyayen abin da za a yi abinci a gida. Yayin da sauran yara ‘yan uwansa ke makaranta.
Hatta a rayuwar makaranta wasu makarantun ba su da wani tsari da zai bai wa yara masu buƙata ta musamman shiga aji tare da sauran yara masu lafiya suna ɗaukar darasi. Haka ma ko a manyan makarantu kamar jami’o’i akwai kasa-kwasan da ba a ɗaukar mai nakasa damar shiga ya yi karatu, sai dai a yi musu canjin sashin karatu zuwa ɓangaren masu nazarin ilimi na musamman.
A bana na samu halartar wata gasar ƙwallon guragu inda wasu ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa suka buga wasan sada zumunci. Na ji daɗin yadda aka tsara abin da yadda cincirindon guragu da kurame, maza da mata suka halarta, cikin farin ciki da nishaɗi, har da raye-raye na murna, domin an basu damar nuna bajintarsu kamar kowa. Na ga wani matashi makaho da yake waƙar hip hop gwanin ban sha’awa, kuma ma fiye da wasu masu lafiyar. Yayin da a gefe guda matasan kurame da ake musu tafinta suke ta nuna fara’arsu da jin daɗin kalmomin waƙar da ake fassara musu.
Lallai yana da muhimmanci mu fahimci cewa, waɗannan mutane ba a son ransu ba ne suka samu kansu a wannan yanayi ba, su ma jarabawa ce suka gamu da ita a wani mataki na rayuwa. Da dama daga cikinsu sun ce lafiya ƙalau aka haife su, amma sakamakon wasu lalurori na rashin lafiya, irin su cutar shan inna, baƙon dauro, kuskuren allura, da tsautsayi yayin tafiya a abin hawa ko wani aiki.
Muhammad wani matashi ne da yake fama da lalurar makanta, wanda ya bayyana min cewa ya gamu da lalurar ne yana shekara ta biyu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda yake neman Digiri a fannin kimiyya, amma wata rana suna ɗakin binciken ƙwaƙwa a makaranta wani sinadari ya shiga masa ido, dalilin da ya sa idanun suka lalace ya zama makaho. Alatilas ya canza karatun da yake yi zuwa sashin koyon aikin jarida, domin an ce masa ba zai iya cigaba da karatun da yake yi a baya ba, a sashin kimiyyar halittu.
Kowa zai iya gamuwa da lalurar nakasa, don haka mu daina nuna musu ƙyama ko ƙasƙanci. Mu tallafa musu su ma su yi rayuwa irin ta sauran mutane. Mu taimaki yaransu da yaranmu masu nakasa, don su girma su zama abin alfahari ga kowa.
