Ranar ’ya’ya mata: Ƙungiyar Rotary ta ɗauki nauyin karatun yara kurame 40

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

A ranar Larabar da ta gabata ne kwamitin ƙarfafa wa ’ya’ya mata da haɗin gwiwar ƙungiyar Rotary da ke Abuja da ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGO) suka ɗauki nauyin karatun da yara kurame 40 da ba su zuwa makaranta.

Ƙungiyoyi masu zaman kansu sun ƙaddamar cigaban ƙwararrun matasa, cigaban ƙarfafawa da LexF H Humanity.

Kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa, ƙungiyoyin masu zaman kansu sun kuma bayar da gudummawar kayayyaki ga ɗaliban.

An bai wa ’yan mata ɗari da ashirin kwamfukar tafi-da-gidanka kowacce, maza 180 kuma an ba su wasu kayyayaki.

An kuma koya wa ɗaliban yadda ake wasu sana’o’i kamar, kwalliya, yin alkaki (cake) da sabulu da dai sauransu.

Dakta Goddy Nnadi, shugaban Rotary District 9125, wanda ya jagoranci ƙungiyoyin masu zaman kansu a ziyarar da suka kai makarantar kurame ta Abuja da ke Kuje, ya ce hakan na daga cikin ayyukan tunawa da ranar yara mata ta duniya.

Ya ce, an kuma bayar da tallafin Naira 200,000 ga makarantar domin baiwa ɗaliban da aka tura daga makaranta saboda rashin biyansu albashin N5,000 kowannensu ya koma makaranta.

Nnadi, wanda ya ayyana buɗe taron, ya ce, an sanar da ƙoƙarin da ake na ganin cewa babu wani yaro, musamman waɗanda ke da buƙata ta musamman da ke zauna a gida ba zuwa makaranta.

Nnadi ya ce, baya ga ɗaukar nauyin, ƙungiyar tare da haɗin gwiwar sauran masu ruwa da tsaki za su gudanar da aikin wayar da kan jama’a a makarantar.

A cewar sa, wayar da kan jama’a za ta taimaka wajen tabbatar da cigaban yaran da kuma abin da za a iya yi domin dawo da jin muryar waɗanda ba su da murya.

Ya yi kira ga ‘yan Nijeriya masu ƙarfi da ƙungiyoyi da su kawo agaji ga makarantu.

Ya ce, “Rotary mutane ne masu tasiri kuma muna nuna shi ta hanyar abin da muke yi.

“Wannan shiri ya fara ne a shekarar 2021 kuma a bana mun yanke shawarar wayar da kan ’ya’ya mata.

“Ana bikin ranar ‘ya’ya ta duniya duk shekara domin gano matsalolin da suka shafi ’ya’ya mata, abin da muke bin su da kuma ƙalubalen da suke fuskanta.

“An kuma ware wannan rana don gano wasu ƙalubalen da ’ya’ya mata ke ƙoƙarin ɓoyewa, wanda hakan zai taimaka wajen magance da yawa daga cikin matsalolinsu.”

Shugaban ya ce, akwai buƙatar a riƙa wayar da kan jama’a akai-akai kan ilimi da ƙarfafa gwiwar ‘ya’ya mata, yana mai cewa suna da matuƙar muhimmanci ga al’umma.

Ya kuma qara da cewa, yaran da suka sha fama da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, fataucin miyagun ƙwayoyi da sauran munanan ɗabi’u, ya kamata a riqa koyar da su yadda za su fitar da kansu daga wannan rayuwar.

Shugabar ƙungiyar ta Rotary International District 9125 na shirin ƙarfafa wa ‘yan mata gwiwa, MLovina Okorn-Ntui, ta ce, ƙungiyoyin rotary sun yanke shawarar ziyartar makarantar kurame domin baiwa ɗaliban damar jin daɗin wannan rana.

Ta ce, “mun yanke shawarar zuwa makarantar kurame ne saboda muna tunanin irin buƙatarsu.

“Muna ta yin tasiri ga rayuwar ’yan matan da ba su da buƙatu na musamman, don haka a wannan karon, mun yanke shawarar yin bikin tare da ’yan matan da ke fama da nakasa da kuma sauran buƙatu na musamman.

“Waɗannan yaran suna buƙatar duk tallafi saboda lamarinsu abin tausayi ne.”

Shugabar ta ci gaba da cewa, “a yayin da na ke magana da ku, muna da ’ya’yan da iyayensu suka jefar a nan saboda halin da suke ciki.

“A gaskiya, akwai wata yarinya da muka ba wa iko a yau wadda mahaifiyarta ta samu shanyewar jiki kuma suna zaune a wani gini da ba a kammala ba.

“Mun sami labarin cewa mahaifin ya jefar da ita a nan ya tafi.”

Ntui ya yi kira ga gwamnati da ’yan Nijeriya masu kishin asa da su kawo agaji ga yara masu nakasa a faɗin ƙasar.

Ta ce, akwai buƙatar dukkan hannaye su kasance wuri guda don taimakawa yaran, ta ƙara da cewa “gwamnati kaɗai ba za ta iya yin hakan ba.”

Ta kuma yi kira ga ɗaiɗaikun mutane da ƙungiyoyi da su yawaita ziyartar makarantu domin tabbatar musu da cewa ’yan Nijeriya na ƙaunarsu duk da halin da suke ciki.

Abdulrazaq Surajo, shugaban makarantar kurame ta Abuja da ke Kuje, ya bayyana jin dazinsa kan tallafin da makarantar ta samu daga ƙungiyoyin rotary da ƙungiyoyi masu zaman kansu.

“Muna godiya saboda ziyarar.

“Waɗannan yaran suna buaƙatar tallafi don kada su ji kamar su ba ’ya’ya ba ne.

“Waɗannan yara ne masu ƙoshin lafiya waɗanda ke da kusan dukkan damar da za su iya badawa wajen gudummawar kason su ga cigaban ƙasa idan an kula da su yadda ya kamata,” inji shi.

Surah ta yi kira da a tallafa musu, musamman a fannin ilimin kwamfuta, kayayyakin more rayuwa da sauran buƙatun ɗaliban.

NAN ta ruwaito cewa, babban abin da ya faru a taron shi ne bayar da gudummawar jakunkuna na makaranta, Unifam, da littattafai da dai sauransu ga ɗaliban.

An kuma gudanar da taron da laccoci kan daƙile shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da lafiyar haila da tsafta.

Har ila yau, laccocin sun mayar da hankali ne kan ilimin jima’i, da fasahar sadarwa ta zamani (ICT) da sauransu.

Makarantar Kurame ta Abuja na da yawan al’umma da ba su gaza 600 ba, kuma tana aiki ne a matsayin makarantar kwana.