Zugacoin na daga cikin kamfanoni ukun kan gaba a harkar kuɗin yanar gizo a duniya – Farfesa Jibia

Daga WAKILINMU

Wani tsohon malami a tsangayar koyar da kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke Kano, Farfesa Aliyu Abdullahi Jibia, ya ce kuɗin kasuwanci na yanar gizo mai suna Zugacoin ɗaya ne daga cikin kamfanoni 3 da suka fi shahara a harkar kuɗin yanar gizo a duniya.

Aliyu Jibia, ya bayyana haka ne a yayin da Jaridar Hausa Daily Post ta yi bikin karrama shugaban gidauniyar Samzuga, wanda ya assasa Zugacoin da Green Zugacoin.

Ya kara da cewa, “Archbishop Farfesa SamZuga, jami’in diflomasiyya ne a tsarin International Society OF Diplomats and Global Emissary Council, wanda shine shugaban tattalin arziki na farko a tsarin IT a duniya.

“Kuma shi ne Farfesa na farko a fannin tattalin arziki a tsarin kuɗin yanar gizo na duniya, kuma farkon wanda ya kafa cibiyar hada-hadar kasuwanci a Afirka.”

Farfesan ya ce, “Zugacoin wanda ya ƙirƙira, na ɗaya daga cikin kamfanoni 3 da suka fi shahara a harkar kuɗin yanar gizo a duniya.

“Archibishop Farfesa Sam Zuga, wanda limamin coci ne a Najeriya da ke zaune a Dubai kuma ɗan kasuwa mai taimakon jama’a, ya samu lambar yabo ta 5 a cikin shirin Doctorate Degree Awards daga jami’o’i daban-daban na duniya, ciki har da wasu jami’o’i a Amurka da Isra’ila.

“Haka kuma, Archbishop Farfesa SamZuga, mamba ne a ƙungiyar ‘yan kasuwa ta Dubai, kuma ɗan Najeriya na biyu da ya karɓi lambar yabo ta Global Citizen a Global Peace Federation tare da hedkwatar ƙasar Koriya da Jakadan Majalisar Ɗinkin Duniya kan zaman lafiya, ta hanyar Global Peace Advocates.

“Hakazalika, hedkwatar Koriya ta Kudu da ke Denmark ta ba shi muƙamin Daraktan kula da harkokin Afirka na kungiyarsu mai daraja.

“Farfesa SamZuga, yana da lasisi a Dubai wanda ke ba shi damar shigo da zinari daga sassan duniya zuwa ƙasar.

“Kuma shi ne na farko a duniya da ya kafa cibiyar kasuwanci ta yanar gizo ta farko mai suna Green don kawo shirye-shiryen sauyin yanayi wanda aka sanar a hukumance a taron sauyin yanayi na Majalisar Ɗinkin Duniya, wanda wannan manufar ita ce kawar da raɗaɗin matsin lamba na rayuwa ga masu ƙaramin ƙarfi,” in ji shi.

Da yake jawabi a wajen bayar da kyautar, Edita kuma jami’in kasuwanci na Hausa Daily Post, Abdulrazak Ahmad Jibia, ya ce an karrama Archbishop Farfesa Sam Zuga dangane da sadaukar da rayuwarsa da ya yi wajen gina rayuwar al’ummar Afirka a ƙarƙashin gidauniyar Samzuga, kiwon lafiya kyauta, koyar da mutane sana’o’in hannu da dai sauransu.

Da hazakarsa na sake gina sashen kuɗin yanar gizo na Zugacoin da Green Zugacoin wanda zai taimaka wajen kawar da talauci a tsakanin al’umma.

A jawabinsa yayin karɓar lambar yabo, Farfesa Mkpa Ogoh Mkpa, wanda ya wakilci Archbishop Farfesa Sam Zuga, ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki da gaisuwa ta musamman ga jaridar Hausa Daily Post, bisa karramawar da aka yi masa, ya kuma tabbatar da cewa Archbishop Farfesa Sam zai ci gaba da yin iya ƙoƙarinsa kuma zai ƙara himma wajen samar da sabbin abubuwa don ciyar da al’umma gaba kamar yadda ya saba.

Taron wanda babban sakataren Gidauniyar Samzuga ta Ƙasa, Alhaji Isah Inuwa Rikoto ya jagoranta a ranar Lahadi, 16 ga watan Oktoba, 2022, a birnin Kano, ɗaya daga cikin tawagar Hausa Daily Post da suka halarci bikin karramawar, Alhaji Ado Ahmad Gidan Dabino MON, wanda ya wakilci shugaban jaridar Hausa Daily Post Injiniya Adamu Attahiru, ya kara zaburar da Archbishop Farfesa Sam Zuga, akan ya kara jajircewa wajen samar da sabbin hanyoyin ciyar da al’umma gaba.