Ƙasar Sin ta taimakawa mutane dubu ɗari dake ƙauyuka a Uganda damar kallon shirye-shirye ta tauraron ɗan Adam

Daga CMG HAUSA

A ranar Asabar din da ta gabata ce, ƙasar Sin ta yi nasarar kammala aikin kafa na’urar kama shirye-shiryen talabijin ta tauraron dan-adam a ƙauyuka 900 dake ƙasar Uganda a hukumance, waɗanda a baya suke fuskantar ƙalubalen hanyoyin sadarwa.

Ministan watsa labarai, sadarwa da fasaha da ba jagoranci na ƙasar Uganda Chris Baryomunsi ne, ya jagoranci bikin miƙa aikin da aka gudanar a ƙauyen Katabi dake gundumar Wakiso a tsakiyar ƙasar.

Ya yaba wa ƙasar Sin bisa tallafin fasaha da take bai wa Uganda.

Yana mai cewa, tallafin zai taimaka wajen samar da ci gaba ga al’ummomin yankin.

A nasa ɓangare, babban jami’in gudanarwa na kamfanin StarTimes dake ƙasar Uganda Aoge Mengdai, wanda kuma ke kula da aikin, ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2018 da aka fara aiwatar da aikin zuwa yanzu, an haɗa ƙauyuka 900 da hidimar kama shirye-shiryen talabijin ta tauraron ɗan-Adam, baya ga fiye da mutane dubu 100 a gidajen iyalai dubu 18 da makarantu dubu 2 da 700, da cibiyoyin kiwon lafiya dake iya kallon shirye-shiryen talabijin ta tauraron ɗan-Adam.

Mengdai ya bayyana cewa, amfanin hidimar kama shirye-shiryen talabijin din, ya zarce shiga talabijin kawai.

Yana mai cewa, a halin yanzu yaran dake waɗannan ƙauyuka, suna iya samun damar koyo ta talabijin da kallon abubuwa ta hotunan bidiyo, wanda ke da matuƙar amfani a harkar ilimantarwa a zahiri.

Bugu da ƙari, za su iya gogayya da sauran makarantu dake wajen al’ummarsu.

Kamfanin StarTimes, kamfani ne na ƙasar Sin dake samar da hidimar kama shirye-shiryen talabijin ta hanyar biyan kuɗi.

Mai fassara: Ibrahim Yaya