Raphael Varane ya yi ritaya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mai tsaron bayan tawagar ƙwallon ƙafar Faransa da kuma ƙungiyar Manchester United, Raphael Varane, ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa ƙwallo.

Ɗan wasan wanda ya lashe kofin duniya a 2018, ya ci wa Faransa ƙwallaye biyar a wasanni 93 da ya buga tun daga 2013.

Wasansa na ƙarshe shi ne wasan ƙarshe na kofin duniya a Qatar 2022, wanda suka yi rashin nasara a hannun Argentina.

“Wakiltar ƙasata na tsawon lokaci shi ne babban karamcin da na samu a rayuwata,” inji Varane.

Ya ƙara da cewa, “a duk lokacin da na saka shuɗiyar rigar nan, raina na cika da alfahari.”

Varane ya ce, “na daɗe ina tunanin ɗaukar wannan mataki tsawon watanni, a ƙarshe na gane yanzu ne lokacin da ya kamata in yi ritaya.”

Varane wanda ya tafi Manchester United daga Real Madrid a Agustan 2021, shi ne na baya bayannan da ya yi ritaya a tawagar Faransa.

A watan Janairu, golan Tottenham kuma kyaftin ɗin Faransa Hugo Lloris ne ya fara ritaya makonni uku bayan kammala gasar kofin duniya.

Varane ne aka yi tunanin zai maye gurbin Lloris a matsayin kyaftin, sai gashi shi ma ya rataye takalmin nasa daga wakiltar Faransa a fagen ƙwallon ƙafa.