Cikin sauƙi Atiku zai lashe zaɓen 2023, In ji Saraki

Daga NASIRU S. GWANGWAZO, Anuja

Wannan wata tattaunawa ce da gidan talabijin ɗin ARISE TV ya yi da tsohon Gwamnan Jihar Kwara kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, Dakta Abubakar Bukola Saraki, inda ya yi bayani mai tsawo kan irin cancantar tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ga shugabancin Nijeriya fiye da sauran abokan takararsa a babban zave mai ƙaratowa na 2023. Blueprint Manhaja ta fassaro muku hirar, saboda irin muhimman batutuwan ƙasa da tsohon Shugaban Majalisar Dattawan ya tattauna a cikinta. Ga yadda tattaunawar tasu ta kasance:

Shin ta waɗanne hanyoyi kake ganin ɗan takarar Shugaban Ƙasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar zai kai ga samun nasara?

Da farko dai, na yi imanin cewa zaɓen shekarar 2023 zai zama tamkar bita ne tare da cimma matsaya a kan irin mulkin da jam’iyyar APC ta yi. Kuma na yi imanin cewa, ƙasa irin tamu wacce take da mutane masu hangen nesa da sanin ya kamata, ba za ta bi bayan gazawa ba. Tambayar da ya kamata ‘yan Nijeriya su yi ita ce: Shin wannan gwamnatin ta jam’iyyar APC ta gaza ko ta yi nasara a sama da shekaru bakwai da ta kwashe tana mulki?

Bari mu yi bita a tsanake na abubuwan sannu a hankali, saboda ina so in yi magana ne tare da kafa hujjoji, ba wai shaci faɗi ba. A shekarar 2015, sun yi wa ‘yan Nijeriya alƙawurra da yawan gaske, ciki har da cewa za su kawo ƙarshen matsalar tsaro, za su bunƙasa tattalin arziki, tare kuma da samar da ayyukan yi ga matasa.

Waɗannan su ne muhimman abubuwan. A shekarar 2015, idan ana iya tunawa, ana fama da matsalar tsaro a yankin Arewa- Maso Gabas, amma tun daga wannan lokacin har zuwa yau, mun ga yadda lamarin tsaro ya taɓarɓare a yankin Arewa- Maso Yammacin Nijeriya. Manoma ba su iya zuwa gonakinsu saboda ana kashe mutane a kuma yi garkuwa da su. Kowa ya shaida rikicin makiyaya da manoma a yankin Arewa ta tsakiya. Haka kuma muna ganin yadda annobar fasa -ƙwaurin man fetur ta ƙaru a yankin Kudu-Maso-Kudu.

Dangane da tsaro, sun gaza, wannan babu tantama. Mu ɗau tattalin arziki, shi ma zan ɗauke shi bi da bi, sannan na ƙalubalance su a kai. Mu ɗau batun karyewar darajar naira. A kan batun tsaro, sun gaza. Bari mu duba tattalin arziki kuma zan sake bin su ɗaya bayan ɗaya in ƙalubalance su a kai saboda duk matakai ne da aka san su matuqa gaya. Bari mu duba tsadar kayayyaki, a yanzu haka ana kusan kashi 16 cikin kashi 100, abin da ba a taɓa gani a zamanin PDP ba saboda bai kai kashi 10 ba. Muna da mafiya yawan ‘yan Nijeriya da suke cikin ƙangin talauci da fatara su fiye da miliyan 33.

Ba haka lamarin yake a can baya ba…

Rashin aikin yi a ƙarƙashin mulkin PDP yana kashi shida zuwa kashi takwas, a yau kuwa yana kashi 33, sai matasa marasa aikin yi da suke da kashi 54. Zuba jari kai tsaye daga ƙasashen ƙetare kuwa, idan mun yi sa’a wataƙila ya kai Dala Biliyan Biyu idan aka kwatanta da Dala Biliyan 9 a lokacin da PDP take mulki. Wannan shi ne zahiri da ko mutum ba ya tsoron Allah ba zai musanta ba.

Me za ka ce a game da halin da tattalin arziki yake ciki?

A tattalin arziki kuwa, a farashin gwamnati, Dala tana a N185, a kasuwar bayan fage kuma N230 a zamanin PDP. A yau kuwa farashin gwamnati shi ne N450 a kasuwar bayan fage N755. Ba a tava ganin hakan ba sai a zamanin APC. Idan ka duba dukkan waɗannan abubuwa, za ka ga cewa APC ta gaza, kuma saboda sun gaza a matsayinsu na jam’iyya, bai kamata mu saka musu da abin qwarai ba. Saboda haka ba na tunanin cewa APC wata abar damuwa ce a wannan gwagwarmaya saboda sun samu damar da za su kyautata jin daɗin ‘yan Nijeriya, amma kayya! Sun ɓarar da damar.

A yanzun tambayar ita ce, wa zai gaje ta? Wasu za su iya cewa ba ma so mu koma PDP. Amma bari mu yi batun komawa PDP. A zamanin PDP kamar yadda na yi bayani, matsalar tsaro ta taƙaita ne ga ɓangare ɗaya kawai na ƙasar nan. A lokacin PDP, bunƙasar tattalin arzikin ta ‘yan Nijeriya tana wajen kashi 8 amma a yanzun dududu ba ta wuce kashi biyu ba, wato ƙasa da ƙaruwar yawan jama’a da ake samu.

A zamanin mulkin PDP da muke magana a kai, ana zuba jari daga ƙasashen waje zuwa ƙasar nan har na wajen Dala Biliyan 8, kuma mu ne muke da tattalin arziki mafi girma a Afirka. Musayar kuɗi ba N700 ta doshi N1000 a lokaci guda ba. A zamanin gwamnatin PDP, kan ƙasar nan ya fi zama a haɗe. Ba sabon abu ba ne a tsari na dimokraɗiyya jama’a su zama suna da zaɓin cewa sun gaji da wata jam’iyya za mu gwada wata.

Amma idan sabuwar jam’iyyar ta gaza, sai ka yi abin da ake cewa da tsohuwar zuma ake magani. Wannan tsohuwar zuma kuwa ita ce PDP ƙarƙashin Atiku Abubakar. Idan ka yi magana a kan sauran jam’iyyun siyasan, idan ka ɗauki ‘yan takaran nasu ɗaya bayan ɗaya, musamman Mista Peter Obi, kada a manta cewa muna gudanar da tsari ne na shugaban ƙasa mai cikakken iko a Nijeriya kuma idan ka je akwatin kaɗa kuri’arka a ranar zave, jam’iyya za ka zava ba Peter Obi ba.

Ba za ka ga Peter Obi ba, jam’iyyar za ka gani. Jam’iyyar da tun a farkon farawa ba ta da ‘yan takara na dukkan kujerun ‘yan majalisa, wanda tamkar shiga motar da ba ta da direba ne saboda ka san cewa ɓangaren zartaswar da na ‘yan majalisun ba za su kasance suna da rinjaye ba.

Kuma wasu za su ce ai sun damu da abin da ake kira sake fasalta tsarin da ake ciki. Waɗannan abubuwa, suna buƙatar sake nazarin tsarin mulkin ƙasar nan. Wanda kuma sai kana da rinjaye a majalisar dokoki ta tarayya.

Masu zuba jari sun daina gamsuwa da umarni da kuma dokokin da ɓangaren zartaswa yake yi; suna so su ga dokoki na ‘yan majalisa da za su mara wa zuba jarin nasu baya. Saboda haka idan ke ƙaramar jam’iyya ce, ba ki da rassa da yaɗuwa da bazuwa kowanne lungun ƙasar nan saboda mun ga haka a 2015 cewa mu yi nesa-nesa da romon baka zuwa zahiri.

Zahirin kuma shi ne APC ta gaza saboda burin jam’iyyar shi ne cin zaɓe, amma ba jam’iyya ce da aka ginata da kyakkyawar aniya ba. Saboda haka ƙaramar jam’iyya da ba ta yaɗu zuwa sassan ƙasar nan ba, ko da tana da shugaban ƙasa, ba ta da ‘yan majalisar dokoki, ba za mu ga abin da ‘yan Nijeriya suke buƙatar gani ba. Dokokin da za su canza tsarin mulki, su sauya fasalin tsarin da ƙasar take gudana, majalisar dokoki ta ƙasa ce kawai za ta iya yi.

Wannan ya kai ni ga batun Atiku Abubakar, a Atiku Abubakar, kana da ɗan takara da tun daga ranar farko, a shirye yake. Za ka ga me nake nake nufi da hakan. Yana da ƙwarewa har a matakin tarayya ba a ɗan ƙaramin yanki ba. Sauran ‘yan takaran biyu kuwa ƙurewarsu ke nan ta sun yi gwamnoni a ɗan ƙaramin yanki. Ni ma na yi gwamna sai dai zan fada muku abin da na sani a matsayina na gwamna tsawon shekara 8, da kuma ƙwarewata a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa, da nake shugabantar ‘yan Nijeriya daga sassa daban-daban na ƙasar nan, harsuna daban-daban, addinai da al’adu daban-daban. Ba ka da wannan ilimi ko ƙwarewa a matakin ɗan ƙaramin yanki na gwamna.

Wasu suna cewa idan mutum yana so ya lashe zaven shugaban ƙasa, dole ya samu nasara a wasu jihohi, kana ganin PDP ta yi isasshen abin da ya kamata ta yi domin yaɗuwar da ake buƙata?

Amsa ce mai sauƙin, PDP a matsayinta ta jam’iyya da take da irin ɗan takaran da muke da shi a Atiku Abubakar, za mu yi sauƙin samun kashi 25 da tsarin mulki ya buƙaci a samu daga sassan ƙasar nan. Duk wani hasashe da tattaunawar da za ka yi a kan haka, za ka ga cewa mun zo na farko ko na biyu. Kudu-maso-kudu yanki ne da PDP take da ƙarfi kuma za mu taka rawar gani sosai a can.

A Kudu -Maso-Gabas, kalubalen da ke gaban mu bai wuce na jam’iyyar Labour Party. Duk da haka za mu taka rawar gani a shiryar mu samu kashi 25 ɗinmu. Za mu taka rawar gani a Arewa-Maso-Tsakiya ma. Haka nan a Arewa-Maso- Yamma da Arewa-Maso-Gabas. Kana buƙatar shiyyoyi huɗu ka lashe zaɓen. Shiyyoyinmi guda huɗu za su kasance Arewa-Maso-Yamma, da Arewa-Maso-Gabas, da Kudu-Maso-Kudu da Arewa-Maso-Tsakiya kuma za mu samu kashinmu 25 a fiye da jihohi 24. Ba wata tantama ko tababa a kan haka.

Sai dai tsarin da kake batu a kai, shi ne ɗan takaran shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party Peter Obi ya ce yana so ya rusa…

Za ka iya watsi da tsohon tsari amma ya kamata ya zama wanda za a fahimta. A ƙasar Faransa, lokacin da Shugaba Macron ya hau, ba ya cikin tsarin sake fasalin, sai dai tafiyar ba ta ɓangaren zartaswa ne kawai ba, ƙasar ta zaɓi ‘yan majalisar dokoki na jam’iyyar ne. Ba wai ina nufin akwai wata matsala da hakan ba ne. Abin da nake cewa shi ne a jam’iyyar an fi ba da fifiko ne ga shugaban ƙasa.

Dole tafiyar ta zama har da majalisun dokoki na jihohi da na tarayya. Jam’iyyar da ba ta da ‘yan takaran majalisun dokoki tun farkon farawa, yana nufin an fara saƙa da mugun zare ke nan. Wannan yana nuna gwamnatin ba za ta gudanar kamar yadda ya kamata ba ke nan. Saboda ba za ta samu goyon bayan da ya kamata a ce ta samu ba, domin iya gudanar da tsare-tsarenta da kuma manufofinta.