Babu wanda ya ƙara farashin man fetur a Nijeriya – NNPC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban kamfanin mai na NNPCL Malam Mele Kyari ya ce babu wanda ya ƙara farashin mai a Nijeriya.

Shugaban ya musanta iƙirarin da wasu ƙungiyoyin masu dakon mai suka yi a baya na cewa an qara farashi.

Mele ya bayyana hakan ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a ranar Talata kan matsalar ƙarancin mai da ake fama da ita a Nijeriya.

Cikin matsalolin da aka ambato da ake ganin su suke kawo tarnaƙi ga man sun haɗa da ɓangaren jigilar man da kuma ɓangaren farashin da aka gaza samun daidaito.

Mele ya ƙalubalanci duka masu ruwa da tsakin da suka halarci taron da su bayyana wanda ya ce musu an ƙara farashin man, ko kuma su gabatar da hujjar sun saye shi a sabon farashin da suka yi iƙirari.

Tun a baya dai ƙungiyar masu gidajen mai masu zaman kansu reshen Kano ta tabbatar wa BBC cewa Gwamnatin Nijeriya ta qara farashin man fetur a hukumance da kashi 8.8 inda a halin yanzu farashin ya koma Naira 185 Legas da kuma 220 a wasu sassa.

A Nijeriya dai an shafe kusan shekara guda ana fama da ƙarancin man fetur da kuma rashin tabbas kan farashinsa.