Wasu ‘yan takara a APC sun bayyana aniyarsu na yin wake da shinkafa a Kebbi

APC

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Waɗansu ‘yan takara ƙarƙashin Jam’iyyar APC a Jihar Kebbi sun bayar da tabbacin za su yi shinkafa da wake a kakar zaɓen nan sanadiyyar cin amanarsu da Gwamna Atiku Bagudu ya yi, a cewarsu.

‘Yan takarar dai sun bayyana rashin jin daɗinsu ne bisa ga rashin tsayar da su da Atiku Bagudu ya yi bayan karɓar milliyoyin kuɗi hannun su bisa ga sharaɗin su ne tabbatattun ‘yan takara, inda aka yi wa Shehu Muhammad Koko takarar kujerar ɗan majaisar wakilai don wakiltar ƙananan hukumomin Koko/Maiyama da kuma Kabiru Labbo Jega a mazaɓar Jega/Aliero da Gwandu duk a majalisar wakilai.

Sun bayyana wannan ne wani bidiyo ta yanar gizo inda suka bayyana cewa sama a zaɓi Bola Ahmed Tinubu, a gwamnan Kebbi kuma a zabi Nasiru Idris NUT, Ƙauran Gwandu, yayin da suka ce kuma a sauran kujeru magoyabayansu su yi zavin ransu.

A wannan faifan bidiyon sun ayyana ba za su ƙyale ba sai sun rama abinda Atiku Bagudu ya yi musu kuma ba za su bar Jam’iyyar APC ba suna nan sai sun ɗauki duk matakin da za su fashe haushin su ga azzaluman da suka zalunce su, a cewarsu.

Yanzu haka dai Jam’iyyar APC a Kebbi ta samu komabaya sanadiyyar wannan hukuncin da Babbar Kotun Ƙoli ta yanke da kuma waɗansu shari’o’i daga Jihar Kebbi wanda ya tabbatar da gaskiyar al’amari da ke nuna yaudarsu ne a ke yi duk inda aka fito.