Kotun Musulunci a Kano ta raba auren Asiya Ganduje da maigidanta

Daga RABIU SANUSI a Kano

Asiya Abdullahi Umar Ganduje wadda ta kasance ‘yar Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ta garzaya kotu ta hannun lauyanta, inda take neman kotun ta kawo ƙarshen auren dake tsakaninta da mijinta, Inuwa Uba, inda ta bayyana cewar za ta mayar masa da sadakin da ya ba ta Naira dubu hamsin.

Da yake yanke hukuncin, Mai Shari’a Malam Abdullahi Halliru, ya ce hujjojin da aka gabatar a zaman shari’ar sun tabbatar da cewar mai ƙarar ta karɓi Naira dubu hamsin.

Sai dai a nasa ɓangaren, lauyan wanda ake ƙara, Umar I Umar, ya yi fatan kotun za ta ba shi dukkanin wasu bayanai na yadda zaman kotun ya kasance, inda ya ce yana da sha’awar za su ɗaukaka ƙara zuwa kotun sama, bayan sun tattauna da wanda yake karewa Inuwa Uba.

A hirarsa da wakilin Blueprint Manhaja, lauyan mai ƙara, Barista Ibrahim Aliyu Nasarawa, ya ce kotun ta raba auren ne bisa tsarin da shari’ar Musulunci ta tanadar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *