Babu mahalukin da nake tsoro, cewar El-Rufai ga manyan Fadar Shugaban Ƙasa

Daga WAKILINMU

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna, ya kalubalancin ’yan Fadar Shugaban Ƙasa da yake zargi da zagon-ƙasa ga takarar Bola Tinubu a zaɓen Shugaban Ƙasa mai zuwa.

Tun a ranar Laraba El-Rufai ya fara tayar da ƙura da zargin cewa akwai jami’an Fadar Shugaban Ƙasa da ke neman yi wa takarar Tinubu ƙafar ungulu.

A wata hirarsa da BBC Hausa, an ji shi yana cewa, “Na rantse babu mahaluƙin da nake tsoro a duk faɗin ƙasar nan.

“Don ana ganin girman mutum ba tsoronsa ake ji ba; amma idan muna girmama mutum sannan yana nuna shi ba babba ba ne, to wallahi za mu sake shi.”

Ana ganin kalaman nasa ƙari ne a kan zargin waɗanda yake zargi a Fadar Shugaban Ƙasa, da ya ce suna neman kai Tinubu ƙasa.

A ranar Laraba, a wata hira da shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels ne El-Rufai ya yi zargin akwai magoya bayan waɗanda suka nemi takarar shugabancin ƙasa a APC wanda Tibubu ya lashe da ke fakewa da Shugaba Buhari domin cimma manufofinsu.

A cewarsa, “Suna so mu faɗi zaɓe saboda haƙarsu ba ta cim ma ruwa ba.

“Suna so mu faɗi zaɓe, suna fakewa da Shugaban Ƙasa da abin da yake ganin daidai ne,” in ji El-Rufai.

A martaninsa, Ministan Yaɗa Labarai da Raya Al’adu, Lai Mohammed, ya ce gwamnati ba ta da masaniyar waɗanda ke wa Tinubu zagon-ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa.

Ya ce Buhari na ɗaukar ɗaukacin ’yan takara da matsai ɗaya, domin ganin an gudanar da sahihin zaɓe kuma yana goyon bayan Tinubu ɗari bisa ɗari.