Daga BASHIR ISAH
Kwamitin Majalisar Wakilai ya zargi Babban Lauyan Tarayya (AGF), Abubakar Malami da jami’an hukumar Interpol kan yi masa katsalandan a binciken da yake gudanarwa.
Kwamitin mai bincike kan badaƙalar satar ɗanyen mai tun daga 2014 zuwa yau, ya ce bai ga dalilin da zai sa jami’an Interpol a bisa buƙatar Ma’aikatar Shari’a suka yi wa wanda ya yi fallasa tambayoyi bayan da Majalisar ta fara gudanar da bincikenta ba.
Kwamitin na bincike a kan zargin da aka kwarmata na sayar wa Chana ɗanyen mai ganga miliyan 48 mallakar Najeriya ta haramtacciyar hanya a 2015 wanda kuɗin ya kai Dala biliyan 2.4.
Sai dai shugaban hukumar ta Interpol ta ƙasa, Garba Umar, ya ce hukumar ta yi aiki ne bisa buƙatar Babban Lauyan Ƙasa.
Shugaban Kwamitin Bincike kan satar mai, Mark Gbillah ya ce, “Akwai wata ƙungiya mai suna Advocacy for Good Governance and Free Nigeria.
“Ƙungiyar ce ta yi wa Babban Lauya wasiƙa tana mai sanar da shi akwai wani gungun masu ɓata suna da ke ƙoƙarin ɓata sunan manyan jami’an gwamnati.
“Me ya sa Babban Lauya zai yi aiki da zargin wanda ba a sani ba?
“Ma’ana shi kansa Babban Lauyan bai tabbatar da gaskiyar kowace ƙungiya ba,” in ji kwamitin.
Kwamitin dai ya nuna rashin gamsuwarsa dangane da bayanin Interpol, inda ya zargi Babban Lauya da yi wa binciken Majalisar katsalandan.
Kwamitin ya kuma nuna fargabansa kan tsaron mai fallasar, tare da jaddada cewa Ma’aikatar Shari’a ta daina neman bayanai kai tsaye daga Interpol, maimakon haka ta riƙa tuntuɓar ‘yan sanda kamar yadda doka ta tsara.
