DAG ta shirya taron hana tarzoma a lokacin zaɓen 2023

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Ƙungiyar wayar da kai a kan hana sayar da ƙuri’a da hana tada tarzoma ta Dispute Resolution And Development Initiative DAG, da haɗin gwiwar (IFES) da taimakon USAID, da UK, sun shirya taron hana duk wani abu na karya doka da tada hatsaniya da kan iya kawo tashin hankali da barazana ko kawo cikas a lokacin zaɓen gama-gari mai zuwa a ƙarshen wannan wata mai zuwa in Allah ya kai mu.

Bayanin hakan ya fito ne daga Sakataren ƙungiyar Muhammad Rabiu Aminu a lokacin da ta shirya taro don wayar da kan matasa da sauran masu ruwa da tsaki a kan harkar zaɓuɓɓuka a matakai daban-daban da ke Nijeriya.

Sakataren na DAG ya ƙara da cewa rikici lokacin zave abu ne da ke kawowa dimukuraɗiyya cikas, “don haka wannan ƙungiya da sauran hukumomi na duniya sun tashi haiƙan wajen ganin ba a samu tashin hankali ba a lokutan zaɓe ko bayan zaɓe domin hakan koma baya ne a tsarin dimukuraɗiyya na kowacce ƙasa.

A ƙarshe Malam Muhammad Rabiu Aminu ya yi kira ga matasa kar su yadda a yi amfani da su wajen shaye-shaye da tada hankali don kawo koma baya a wannan ƙasa, inda kuma ya buƙaci ‘yan siyasa da su sa kishin al’umma da kishin ƙasa da kuma cika alƙawari na inganta rayuwar al’umma.

Mahalatta taron da wasu ‘yan ƙungiyar ne da dama su ka yi jawabi na gamsuwa a taron na DAG.