Kotu ta yanke wa wasu tsoffin jami’an SARS hukuncin kisa ta hanyar rataya

Daga BASHIR ISAH

Babban Kotu mai zamanta a Fatakwal ta yanke wa wasu tsoffin jami’an Runduna ta Musamman Mai Yaƙi da Fashi da Makami (SARS) su biyu hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Kotu ta yanke musu hukuncin ne bayan da ta kama su da laifin aikata kisa.

Idan ba a manta ba, a baya an gurfanar da jami’an SARS biyar da suka haɗa da ASP Samuel Chigbu, Shedrack Ibibo, Magus Awuri, Ogoligo da kuma Olisa Emeka kan kisan wani Michael Akor da Michael Igwe a lokacin da suke tsare da su bisa zargin satar katin waya a yankin Ƙaramar Hukumar Oyigbo a 2015.

Amma ya zamana Samuel Chigbu da Ogoligo sun mutu a gidan yarin Fatakwal sannan aka ci gaba da shari’ar Shedrack Ibibo, Magus Awuri da Olisa Emeka.

Da take yanke hukunci, Alƙalin kotun, M.O Opara, ta kama Shedrack Ibibo da Magus Awuri da laifin haɗin baki, kana ta wanke Olisa Emeka.

Da take yi wa manema labarai ƙarin haske game da hukuncin, lauyan mai tuhuma ta nuna farincikinta dangane da hukuncin da kotun ta yanke, tana mai cewa adalci ya yi aikinsa.

Ta ƙara da cewa, hakan zai zama darasi ga sauran jami’an ‘yan sanda da kuma sanyaya wa ‘yan uwan waɗanda aka kashen rai.