‘Ku ba ni kwana 7 zan magance ƙarancin kuɗi’ – Buhari

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ba shi kwana bakwai domin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin kuɗin da ake fuskanta a ƙasa sakamakon canjin kuɗin da CBN ya yi.

A wata sanarwa da ya fitar, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Femi Adesina, ya ce Buhari ya bayyana haka ne yayin ganawarsu da ƙungiyar gwamnoni ta Progressive Governors Forum ranar Juma’a a Fadar Shugaban Ƙasa.

Gwamnonin sun ziyarci Buharin ne domin tattauna mafita dangane da ƙarancin kuɗin da ake fama da shi a ƙasa baki ɗaya wanda a cewarsu lamarin na barazana ga manufar bunƙasa tattalin arzikin da gwamnati ke da ita.

A cewar Buhari, sake fasalin wasu takardun Naira da aka yi hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa da kuma janyo amfani na tsawon lokaci.

Sai dai ya nuna shakku kan ƙoƙarin bankuna wajen cim ma nasarar matakin da aka ɗauka.

“Wsu bankunan ba su taɓukawa, kansu kawai suka sani.

”Ko da wa’adin shekara guda aka ƙara, matsalolin da ke da nasaba da son kai ba su gushewa,” in ji Buhari.

Ya ce ya gani a rahotanni yadda ake fama da ƙarancin Naira, tare da ba da tabbacin kwanaki bakwai da suka rage daga 10 da aka ƙara zai yi amfani da su wajen daidaita lamurra.

By Editor