Sauyin kuɗi ya jefa ‘yan kasuwa a matsanancin hali – Sani Isah

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An yi kira ga gwamnati musamman Babban Bankin Ƙasa CBN akan a wadata al’umma da sabbin takardun kuɗi don rage matsanancin wahala da ake ciki.

Shugaban rukunin Kamfanin Sani Asiya, Alhaji Sani Isah ne ya yi kiran da yake zantawa da ‘yan jarida, inda ya ce tunda ‘yan kasuwa suke a ƙasar nan basu taɓa tsintar kansu a hali irin wannan ba, kasuwa ta zama kamar a raba ƙwallo saboda mutane da ya kamata su zo su yi sayayya babu kuɗi a wajensu.

Ya yi nuni da cewa akwai mutane da yawa da ba su da asusun ajiyar banki bare ya samu katin fitar da kuɗi. hatta shi akan kansa ba shida katin.

Ya ce wannan wani abu ne da aka zo da shi bakatatan, “yanzu ace za ka sai goro na N100 a ce sai kasa a asusun banki? akwai wahala abu ne da ba a saba da shi ba sai yanzu yazo.”

Dama abinda suka so a ce gwamnati ta bada lokaci da za a samu a gane yadda abin yake, amma abu da gaggawa haka, a gaskiya ya jefa kasuwancinsu a matsala, inji shi.

Ya ce da an bada lokaci kuma an wayar da kan mutane ana kuma janye kuɗin a hankali to mutane ba za su shiga yanayi irin wannan ba.

“Amma janye kuɗi lokaci ɗaya shine ya ruɗa mutane kowa ya fito da abinsa ya bayar, saboda gudun kar abin ya jawo masa asara.”

Alhaji Sani Isah Asiya ya shawarci gwamnati ta duba Allah ta sassautawa mutane ta fito da sabbin takardun kuɗin nan a wadata su.

“An ce ka je banki a baka 20,000 wani magidanci kullum na kashe 100,000 a gidansa. Mutane da yawa masu ƙananan sana’o’i ba su da asusu an zo an ce kowa sai ya maida ku dai banki, an mayar ba sabbin a ƙasa, abinda ya kamata a tuttuɗo sabbin su shigo kasuwa,” a cewarsa.

By Editor