Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Fadar Shugaban Ƙasa ta mayar da martani kan hasashen cin hanci da rashawa na Ƙungiyar Transparency International (TI), wanda ya nuna cewa, Nijeriya ta samu koma-baya a yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu na Nijeriya, Alhaji Lai Mohammed, ya na mayar da martani ne a kan kare gwamnatin Jam’iyyar All Progressives Congress a ranar Laraba, jim kaɗan bayan kammala taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.
A cewar Lai Mohammed, yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ba wai don a farantawa ƙungiyar Transparency International ake yi ba ko kuma ya yi mata daɗi ta kowane fanni.
Idan za a iya tunawa, Transparency International ta hannun wakikinsu a Nijeriya, Cibiyar kare haqqin jama’a ta Civil Society Legislative Advocacy Centre CISLAC ta ce Nijeriya ta ragu daga matsayi 150 zuwa 154 a ƙididdigar cin hanci da rashawa a duniya a shekarar 2022.
Ya danganta ne da batutuwa da dama da suka haɗa da ‘yantar da ɗaiɗaikun mutane, musamman ‘yan siyasa da aka ɗaure a gidan yari saboda ayyukan rashawa. Hukumar cin hanci da rashawa ta duniya ta kuma yi ƙiyasin kimarta game da rashin gaskiya a cikin kasafin kuɗi da aiwatarwa, gami da almubazzaranci na gudanarwa a ɓangaren jama’a.
Ministan Yaɗa Labarai da Al’adu ya kuma zargi ma’aunin na TI, yana mai nanata cewa yaƙi da cin hanci da rashawa ba wai kawai a kama ko a gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata irin waɗannan laifuka ba ne.
Ya ce, “Game da tambaya kan ƙididdiga na Transparency International na Nijeriya, matsayarmu guda ne. Ba muna yaƙi da cin hanci da rashawa ba ne domin muna son burge Transparency International ko wata kungiya ko wani ba.
“Muna yaƙi da cin hanci da rashawa ne saboda mun yi imanin idan ba mu yaƙi cin hanci da rashawa ba, ba za a samu ci gaba ba ta fuskar tattalin arziki ko ma a siyasance. Don haka, abin da muke yi da abin da muke sanyawa don yaƙar cin hanci da rashawa ba don wani ya ƙi mu ba ne.
“Duk da haka, zan iya tabbatar muku cewa ba mu san wane irin ƙididdiga TI ke amfani da shi ba. Duk wata ƙididdiga da suke amfani da shi a fili ya gafala daga abin da wannan gwamnatin ke yi, don yaqi da cin hanci da rashawa.
“Yaƙi da cin hanci da rashawa ba wai mutane nawa kuka kama ba? Mutum nawa kake ƙoƙarin kamawa? Mutane nawa ka yanke wa hukunci? Tabbas ko a wannan ɓangaren, muna da tarihi mai matuƙar burgewa, shin EFCC ce ko ICPC? Kuna da alama, idan kun kalli abin da muke yi har ma don yin ayyukan ɓatanci, kusan ba zai yiwu ba ko kuma abu ne mai wahala…
“Zan ba ku misalai biyu kawai, alal misali, gwamnatin nan lokacin da aka dawo da kuɗaɗen da Abacha ya wawure, aka qwato wasu kuɗaɗe daga USD, UK da Turai, abin da wannan gwamnatin ta yi shi ne, maimakon a biya waɗannan kuɗaɗe.
Baitul malin kuma ta fuskanci yiwuwar sace su ko kuma a sake dawo da su, gwamnati ta yanke shawarar cewa za mu sanya waɗannan kuɗaɗe a cikin wani asusu na daban, mu kuma nemi asusun saka hannun jari na qasa da ya sarrafa waɗannan kuɗaɗe, kuma mun yi amfani da waɗannan kuɗaɗe wajen gudanar da wasu ayyuka na musamman.”
