Rashin tawakkali da dogon buri ke sa wasu mata cin bashi

Daga SADIYA GARBA YAKASAI

Yau maganarmu ta na da matuƙar muhimmanci ga mata har ma maza. Rayuwa ta canza da yanzu mata sun mai da cin bashi kamar sana’a tunda har guruf-gururf gare su.

Mata sun manta rayuwa ba duniya kaɗai za mu zauna ba. Su na saka iyaye da dangi da miji da yaransu cikin wahala. Wallahi, abun takaici ne a ce matarka ko ɗanka yana wannan ɗabi’a ta zubar da daraja, saboda  kawai ɗora wa kai masifa. Ba fa dole ne sai kin yi abunda baki da shi ba, don wannan rayuwa yanzu kowa na kansa yake nema.

Nauyi: Wasu matan na kukan mazajensu ne suka sa su cikin wannan musiba, wasu kuma kawai ɗora wa kai ne. Baki rasa ci ba da sha ba, to me zai sa dole sai kin debowa kanki tashin hankali. Yau ki ci a nan, gobe a can. A zo har gida ana tozarta ki gaban mijinki da yaranki, ko gaban iyayenki, da ƙannenki mata da maza.  Wannan wacce irin ƙaddara ce?

Ya kamata maza su dage da koya wa matansu haƙuri da kau da kai. A yi musu bayanin rayuwa da yadda take. Duk da wasu mazajen su ma da sa hannunsu matan ke ɗebo bashin. Eh mana, ka fita baka ba da na safe ba, ba na rana, ga dare. Ga babu sabulun wanki, ba na wanka, abinci ma ba ka wadata su da shi ba. Don me uwa ba za ta shiga sabgar ɗauko maka magana ba? Tunda zuciyar uwa tana da taushi, babu uwar da za ta ga yaranta suna kukan yunwa, ta sa ido tana kallon su. Dole ta fita ta nemo.

Idan ba haka ba, ƙofa guda biyu ta buɗe ta tarwatsewar gidan ka.  Na farko, za ta iya ɗauko bashi ko na waye,  sannan kuma za ta iya faɗawa wata hanyar banza ba tare da ta yi tunani ba. Sai daga baya, abun zai zamo muku tashin hankali. Da yawa aure ya mutu a dalilin ɗaukar bashi.

Rayuwar matarka da yaranka na cikin gararin muddin ba za ka fita haƙƙin iyalanka ba. Kuma wallahi gidanka ya kama wuta. Uwa ta fita cin bashi, ɗanka ya shiga shaye-shaye da ‘yan sace sace. Shikenan ka zama sai ido, ba ka san yadda za ka yi ba saboda kai ma  zuciyar ka ta mutu. Idan ɗiya mace gare ku, ita kuma ta faɗa hanyar bin maza. tunda an gaza biya mata buƙata, ka gaza kuma ka sa musu ido. Uwarsa ta fita ta samo har kai a zauna a ci, kai fa gari ya waya, dole kana da laifi.

Wai maza ba kwa zuwa kotuna kuna ganin yadda ake kai mata yan bashi? Wasu a daure su in ba su ba da ba, wasu su biya, amma mutunci ya zube, wasu a kai su kurkuku.  ga shi nan dai aikin kenan. Ya sallam! Me ya sa ba mu da lissafi ne? Da zarar ka ga mace ta fara haka, to zaunar da ita ka ji damuwarta.

Masu ba da bashi: Da hannunsu cikin wannan abu. Don me za ki ba wa mace bashin da kika san ba za ta iya biya ba? Eh mana, idan ba don son rai ba, da ganin macen da za ta iya biyan bashi ta fita dabam. Amma ke kawai don za ta ɗora miki riba, sai kawai ki kwashi kayan ɗaruruwa ki ba wa mace wai ta biya ki kafin wata uku ko hu]u. Ya ilahi! wannan wacce irin toshewar basira ce, da za ki ɗebi kaya ko kuɗi,  ki ba ta ki yi tsammanin za ku wanye lafiya? Gaskiya ganganci ne, da wasa da hankali. Shi ya sa abubuwa suke ƙara caɓewa.

An yi kitso da kwarkwata: Ta wani fannin kuma, mazan ne ke tura matan nasu su ciyo bashin . Idan kuma ta kwaɓe, su bar matan ciki da tarin wahala. daga ƙarshe, kotu ce za ta raba faɗan, ko a ɗaure mace. Kin rasa kuɗin,  ko kuma a yi beli, ta dinga kai kuɗi duk ƙarshen wata. Asara ta same ki, ba kuɗin ba daraja. Don kuɗin tare da masu Shari’a za a raba, kun yi biyu babu.

Da maza za su rika fita haƙƙin iyalansu yadda Shari’a ta ce. Da ba za a samu yawaitar masu bashi ba. Da mata za su haƙura da iya abunda Allah ya ba su da ba za su fuskanci tozarci da wahala ba, don Allah mata muyi wa rayuwa uzuri.

Tawakkali:  Yana da kyau mata Mu sa tawakkali a zukatanmu don bawa da arziki duk na Allah ne. Ba sai mun tura kanmu ga halaka ba. Babu mutunci da daraja a ce mu mata muna zuwa karɓar bashi a ko’ina har ta jawo ana mana tijjara a Duniya. Maza kuma su dage su fita haƙƙin matansu da yaransu yadda kowa zai ji da]in zama.

Don mu duk amana ne a gun  junanmu. Mu rufa wa juna asiri don yi wa yara tarbiyya don Allah. Ba a tara arziki ta dole, idan lokaci ya yi shikenan ba sai mun jagula wa kai zukata ba. Babu wata gwaninta a cin bashi. Kuma ba mu da hurumin cewa wai tarbiyya muke koya wa yara.

Batu na gaba shi ne, yadda uba ke sa ido kan harkar iyalinsa, amma ba ya magana. Wannan ba daidai ba ne, shi ]an yau sai da sa ido . duk yadda ka so da takurawa ko duka duk ba sa hana yara fitina. Gara ma nuni da nasiha. Idan yau ka yi ba a ji ba, gobe za a ji. Don haka,  iyaye mu sa wa yara ido kan sha’anin rayuwarsu. Iyaye mata, yanzu fa Duniya dai ta canja.

Abu ma fi muni da ciwo, yadda ake wa yara ƙanana fyade. Wasu a cikin gidan iyayensu ma ake musu saboda sakaci, wasu kuma a waje ake lalata su. Kuma babu yadda iyaye za su yi. Saboda wallahi da kanmu iyaye mu ke kiran masifa ƙiri-ƙiri mun san masu aikatawa, amma saboda sakaci sai mu ja baki mu yi shiru, gudun kada Duniya ta sani. Duk da yanzu ba a Shari’a ta gaskiya, amma yana da kyau mu sanya ido.

Wallahi masu irin wannan rayuwar su ji tsoron Allah, su tuna za mu mutu, mu koma ga Allah. Kuma komai ka yi za a nuna maka. Kuma da kyawawan ayyukanka za a biya, to meye ranar hakan? Ba sai an je can ba ma, tun daga Duniya za ka fara ganin sakayyar abunda ka shuka mai kyau ko mara kyau, balle zuwa can.

Ka lalata ‘yar wani ka ce za ka ga alheri? Wallahi ba haka ba ne, da sannu za ka tarar da aikin ka.duniya dai ba gidan zama ba ce. Yadda muka zo ba mu santa ba, haka za mu koma ba tare da mun sani ba. Saboda haka, mu ji tsoron Allah.

Insha Allahu za mu ɗora daga inda muka tsaya. Allah ya nuna mana wani satin lafiya. Ƙofarmu a buɗe take; gyara ko shawara ko tambaya. Na gode.