‘Yan bindiga sun yi garkuwa da iyayen Kakakin Majalisar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da yin garkuwa da mahaifi da kishiyar mahaifiyar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Nasiru Muazu Magarya, a wani hari da ‘yan bindigar suka kai a ƙauyen Magarya da ke cikin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar

Mai magana da yawun rundunar, SP Shehu Muhammd, shi me ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Hussaini Rabiu ya tura isassun jami’an tsaro da nufin ceto mutanen da aka sace.

Sai dai wani mazaunin yankin mai suna Muhammadu Lawali, ya shaida wa wakilin MANHAJA ta waya cewa, ‘yan bindigar sun kai hari garin Magarya inda nan ne garin Kakakin Majalisar da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Laraba inda suka sace mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa da kuma wasu mutum huɗu.

Lawali ya ce, “‘Yan bindigar sun kuma kai irin wannan hari kan al’ummomin ƙauyukan Kaiwa Lamba da Jinkirawa da kuma Sabon Fegi.”

Lawali da sauran al’ummar yankunan da harin ya shafa, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Zamfara da su gaggauta ƙara yawan sojoji zuwa yankin don kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwar da su daga hannun ‘yan bindigar da ma daƙile harkokin ‘yan taladdan a jihar baki ɗaya.