Tsohon gwamnan Kano da Binuwai, Dominic Oneya ya rasu

Bayanai daga jihar Delta suna tabbatar da rasuwar tsohon gwamnan jihar Kano da Binuwai na mulkin soja, Dominic Oneya.

Oneya ya rasu ne a Larabar da ta gatabata a garinsu Agbarho, jihar Delta.

Majiyar jaridar Solacebase ta ce, marigayin ya rasu ne bayan da ya yi fama da rashin lafiya.

An haifi Dominic Obukadata Oneya ne a ranar 26 ga Mayun 1948 a yankin ƙaramar hukumar Apapa a jihar Legas.

A halin rayuwarsa, marigayin ya yi gwamna a Jihar Kano a ƙarƙashin mulkin soja daga Augustan 1996 zuwa Augustan 1998 a zamanin mulkin marigayi General Sani Abacha.

Kazalika, ya riƙe jihar Binuwai daga Augustan 1998 zuwa Mayun 1999 ƙarƙashin mulkin General Abdulsalami Abubakar, inda ya miƙa mulkin jihar ga zaɓaɓɓen gwamna na wancan lokaci, wato George Akume, a ranar 29 ga Mayun 1999.

Haka nan, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Nijeriya (NFA).