Tsohon Mataimakin Sufeto-Janar, Nuhu Aliyu ya rasu

Tsohon Mataimakin Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda, Nuhu Aliyu, ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a Kaduna bayan fama da rashin lafiya, in ji wata majiya ta kusa da mamacin.

Aliyu haifaffen garin Kontagora ne a jihar Neja, kuma an haife shi ne a Yunin 1941.

A halin rayuwarsa, Aliyu ya yi sanata har na wa’adi uku, wato a 1999 da 2003 da kuma 2007, inda ya wakilci yankin Neja ta Arewa a Majalisar Dattawa.

Ya riƙe muƙamin Shugaban Kwamitin Harkokin ‘Yan Sanda na Majalisar Dattawa daga1999 zuwa 2003.

Kafin ya yi murabus daga aikin ɗan sanda, sai da ya da ya taki matsayin Mataimakin Sufeto-Janar (DIG) mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar.

Aliyu ya rasu ya bar ‘ya’ya shida, sannan ya shekara 80 a duniya.