Zulum da Shettima sun ziyarci Abba Kyari?

An bayyana cewa Gwamna Umara Babaga Zulum na jihar Borno, da gwmanan Borno na dauri, Sanata Kashim Shettima, ba su san hanyar zuwa gidan DCP Abba Kyari ba balle kuma su ziyarce shi.

Mai magana da yawun Zulum, Malam Isa Gusau shi ne ya bayyana haka don ƙarin haske kan ji-ta-ji-tar da aka yaɗa cewa jagororin biyu sun ziyarci Kyari a gidansa.

Gusau ya ce ya zaɓi ya yi magana kan batun ne tun da shi Abba Kyarin bai fito ya yi wa duniya bayani game da batun ba kamar yadda ya yi alƙawari.

Isa Gusau ya ce wasu makusantan Abba Kyari ne suka ɗauki bidiyon ziyarar da Kyari ya kai wa Sanata Kashim a gidansa da ke Abuja a ranar 30 ga Yunin 2021 don yi masa fatan alheri game da labarin ƙarya kan mutuwarsa a Turai da wasu mahassada suka yaɗa.

Bidiyon da shi ma kansa Kyarin ya yaɗa a shafinsa na facebook jim kaɗan bayan ziyarar tasa ga Shettima.

Kyari ya ziyarci Shettima ne don yi masa fatan alheri kamar yadda sauran masoya da dama suka kwatanta a wannan lokaci.

Gusau ya saki wani bidiyo da ke nuna yadda masoya suka ziyarci Shettima a gidansa don jajanta masa kan labarin ƙarya da aka yaɗa game da mutuwarsa, wanda wannan gida ne mahassadan suka bayyana a .atsayin gidan Kyari.

Gusau ya buƙaci shi ma Kyari ya aikata kwatankwacin abin da ya aikata don wayar da kan jama’a kan batun kamar yadda ya yi alƙawari kasancewar shi da kansa ya yaɗa bidiyon a shafinsa na facebook.