Rayuwa a Nijeriya

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Tun kafin na fara wannan rubutu na ga wani rubutu a yanar gizo da ke baiyana cewa farashin koda ya tashi don yanda wataƙila wasu ’yan Nijeriya kan garzaya asibitoci ko kasashen ƙetare don sayar da kodar su, hakan ya sa su samu na kalaci. Ai ba mu manta labarin tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Ike Ekweremadu ba wanda a sanadiyyar yadda wani matashi da su ka kai Turai da matar sa don a cire kodarsa a sakawa ’yarsu da ke buƙata ya sa lamarin ya juye inda a yau Ekweemadu ke gidan yari.

Babbar hanyar samun kuɗi ne kuma har ma akwai rahotannin yadda wasu kan shiga asibiti don a duba su kan wani ciwo sai ta kai ga an cire mu su ƙoda. Akwai misalin samun wanu likita da zargin cirewa wata mata ƙoda a jihar Filato.  Labarin ya nuna an duba matar inda daga bisani sabon ciwo ya taso har daga bisani a ka gano abun da ya faru. Masana lamuran kasashen ketare da waɗanda su ka yi tafiye-tafiye sun ba da labarin yadda ‘yan Nijeriya kan sayar da ƙodar su a Turai inda su kan samu maƙudan kuɗi. Shin wasu ‘yan Nijeriya da ta kan kai su ga sayar da ƙoda don samun kuɗi me ke janyo msu su hakan? Shin neman kuɗin biyan buƙata ne a lokaci ɗaya ko neman maganin talauci don yanayin matuƙar tsadar rayuwa a ƙasar?

Ko ma me za a ce abun damuwa ne ainun a kasa mai albarkatun ma’adinai, noma da kiwo a riƙa samun yanayi mai ban takaici har akasarin talakawa kan kwana ba tare da sun samu abinci ba. Arziki dai ga shi nan birjik a ƙasar. Hatta yadda a ke samun cin hanci da rashawa ko babakere a kan dukiyar talakawa ka ji a na maganar sace biliyoyin Naira amma ƙasar ta rage sauran kuɗi da wani ma marar gaskiya zai hau madafun iko shi ma ya kwashi na sa! Haƙiƙa duk wanda ya lura da wannan ya san Nijeriya na da dimbin arziki. Abun da ya ragewa Nijeriya shi ne samun jagoranci ta yadda kowa zai amfana da dukiyar ƙasar. Abun mamaki ne ainun a ce har yau labarin ba magani a asibiti, ba ruwan sha mai tsabta ko tituna masu kyau shi ne kan gaba a lokacin kamfen. Ya nuna fa ba a cika alƙawarin da a ke ɗauka ne. Ba dukkan ƙasar ne za a ce ba kowane abun more rayuwa ba amma a gaskiyar magana akasarin talakawa na rayuwa ne a yanyin hannu baka hannu kwarya. Muhimman abubuwa uku a rayuwa in ba su samu ba akwai ƙalubale, muhalli, abinci da sutura.

Duk mutumin da ya rasa daya daga ukun nan ya na cikin takaici. Mu tambayi kan mu yau a Nijeriya cikin abubuwan nan uku nawa ne mafi yawan mutane ke da su? In an bincika sosai za a samu akwai waɗanda ba su da ko daya daga muhimman abubuwan. In an samu abinci ko ba nama ba laifi, in an samu riga ko ba aiki a jikin ta matuƙar za ta rufe jiki da sauƙi, in an samu muhallii inda akalla mutum zai samu rufi a kan sa da zai tare rana da ruwan sama da sassauci. A Abuja na tattauna da wani direba da ke cewa akwai waɗanda ke rayuwa a cikin motar su. Ma’ana su kan yi aiki da rana in dare ya yi su samu wani bigire su kwantar da kujera su kwanra. Wanka da sauran buƙatu kuma akwai bayan gida na kyauta ko a shiga manyan masaukan baƙi a a yi kamar an zo duba wani ne daga nan a shige ɓangaren kama ruwa na baki.

Rayuwa ta zama cikin dabaru. Ga kuma dan Karen tsadar rayuwa inda aƙalla mutum na buƙatar dubbai kullum don sayan marar tuwo. Buge-buge in bai kawo wuta ba sai ka ga mutum ya na gallafiri tsakanin gaskiya da akasinta. A kan gabatar da kasafin kuɗi duk shekara ka ji a na bayanan hanyoyin da za a samu kuɗi da yadda za a raba shi, a ƙarshe sai shekarar ta kare ba tare da akasarin jama’ar ƙasa sun samu gajiya ba. Ina ma a ce ko da ƙuncin rayuewa akwai tsaro ta yanda mutum zai shiga dakin sa ya kwanta ido biyu a rufe. In an samu haka da sauƙi. Yayin da a ke ta laluben hanyoyi na kawo ƙarshen barayin daji sai mu ka ji ga wasu masu suna Lakurawa sun bayyana a arewa maso yamma su na kisan gilla.

Bayan an yi ta tambaya su waye Lakurawa sai mu ka samu labarin dama su ma su na nan amma a wani salo daban ba na aukawa jama’ar gari ba. Na ji an ce daga ƙetare ko ƙasar Mali su ke shigowa kuma hatta ɓarayin daji na tsaron su don su na da muggan makamai da duk wanda su ka fuskanta kashin sa ya bushe. Karin bayanai na nuna su na ɗabi’u ne tamkar yadda farko ‘yan boko haram su ka yi kamar masu wa’azi da kawo lamura masu tsauri da bah aka su ke ba a addini. Lakuwara kan cire limami in sun ji bai gwanance da Larabci ba.

Ya nuna an dauki mutanen kamar na Allah ne sai yanzu su ka baiyana ƙarara ‘yan ta’adda ne. Fakewa da addini da zubar da jinin jama’a na nuna addinin a ke bi ba. Bisa wannan dalilin a ke caccakar hukumomi da rashin ɗaukar mataki na kashe matsala tun ta na karama. Daga targaɗen ɓarayin daji a arewa maso yamma yanzu a ce ga kashe-kashe daga Lakurawa. Ina mutane za su sanya kan su ne tun da ba damar yin noma balle kiwo. Rayuwa a Najeriya kuma ba zai yiwu a ce mutum ke kula da tsaron ran sa ba ko garin sa ba. Har yanzu dole a tunawa gwamnati cewa hakan haƙƙin ta ne kuma shi ne ma kan gaba a ayyukan da ya dace ta mayar da hankali a kai. In an samu tsaro a nana ne za a koma kan sauran lamuran yau da kullum.

Gwamnatoci a dukkan matakai ya dace su ɓullo da hanyoyin samun arziki daga albarkar da Allah ya horewa ƙasar ta mu.

Za mu raba irin dibino miliyan mai yi sau 2 a shekara – Hukumar Yaƙi da Hamada;

Hukumar kafa shingen yaƙi da hamada ta Nijeriya GREAT GREEN WALL ta ce za ta raba irin dibino miliyan 5 mai samar da yabanya sau biyu a shekara.

Wannan dai na daga cikin muradun samar da bishiyoyi don cin ribar samun kuɗin shiga da kuma yaƙi da dumamar yanayi.

Hukumar da ke aiki a jihohi 11 da ke fama da barazanar hamada a arewacin Nijeriya na yayata kamfen din samun aƙalla kowa ya dasa bishiya ɗaya ya kula da ita har ta samar da kariya da inuwa.

Shugaban hukumar Saleh Abubakar ya ce an samo irin kuma duk wanda ya samu shi zai riƙa samun makudan kuɗi “kiyastawa da mu ka yi yanzu irin dibinon da za mu raba a kakar shuka da za mu shiga za a samun biliyan 260 a shekara na Naira. Wanda ya samu kamar 20 zai iya samun Naira miliyan daya a wata”

Game da tsarin nan na dasa bishiyoyi da samun biya daga ƙasashen ƙetare CARBON CREDIT, Saleh Abubakar ya buƙaci jama’a su kafa ƙungiyoyi don yin aiki da hukumar wajen samun kasafin “a hada ƙungiyoyi, a haɗa ƙarfi da ƙarfe kowa ya fito mu yi abun tare. Kuma kowa ya yi ƙoƙari ya yi lambu a cikin gidansa inda zai riƙa samun kayan miya”

Gwamnatocin jihohi da ƙungiyoyi kan ƙaddamar da dashen bishiyoyi amma ba lallai ne su samu kulawa ba bayan kammala biki.

Lamarin dausayin yankin arewa ya hada da kogunan da hamadar ke kafar da su musamman a lokacin rani.

“Suna na Musa Bala Yakasai, ni ne ‘National Coordinator’  na ‘Arewa Green Moɓement’ Akwai wani abu da a ke kira a turance ‘RIɓER BANK’ shi Kogin Hadeja  da Jama’are ya taho ne daga yanki da ya haɗa da tafkin Chadi. Don haka sai an yashe kogin Hadeja da Jama’are kafin ruwa ya gudana yadda ya dace. Manoma su samu gabban ruwa har waje ya yi tsirrai ya zama kore shar.”

Sare bishiyoyi don samun itacen girki bai dakata ba duk da samun zabin hanyoyin iskar gas da wa imma ba rahusar amfani da su a karkara ko wasu na ɗari-ɗarin amfani da zabin don gudun gobara.

Kammalawa;

Da wannan za mu iya fahimtar cewa Nijeriya tamkar kaza ce da kan kwan kan dami amma ba ta sani ba. Ko kuma zai iya yiwuwa kazar ta sani amma saboda rashin dabarun iya amfana da damin sai ta kwana ta na hamma. Yakan iya yiwuwa kuma ga damin amma ba a buƙatar akasarin jama’a su amfana da shi. Ga hanyoyi masu sauƙi da za a iya raba arziki a ƙasa da ke buƙatar jagoranci a dukkan matakan gwamnati. Mu na addu’ar Allah ya dawo ma na da irin ‘yan kishin ƙasa da su ka karɓo ‘yanci a 1960 su dawo ta hanyar wasu masu kyakkyawaralkibla don jagoran Nijeriya ta yi bankwana da talauci.