
Kotun Tarayya a Abuja ta sanya ranar 3 ga Yuni domin fara sauraron ƙarar da Nafiu-Bala Gombe ya shigar kan rikicin shugabancin jam’iyyar ADC.
Nafi’u-Bala Gombe na neman kotun ta hana David Mark, Rauf Aregbesola da wasu shugabannin rikon kwarya na jam’iyyar cigaba da bayyana kansu a matsayin shugabanni.
Ya kuma yi zargin cewa tsarin shugabancin ya saba wa kundin tsarin jam’iyya da dokar zaɓe kamar yadda jaridar Daily Trust ta tabbatar.
Rahotanni sun nuna cewa an riga an tura sanarwar kotu ga dukkan bangarorin da ke shari’ar, yayin da aka mayar da shari’ar zuwa Mai Shari’a Peter Lifu bayan ɗaukakar wani alkalin da ya gabata zuwa Kotun Daukaka Kara.
A halin yanzu, kotun ta tabbatar da cewa za a fara sauraron shari’ar a ranar 3 ga Yuni domin yanke hukunci akan al’amarin.
