Rikicin APC: NWC ya kafa kwamitin bincike da sassantawa

Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na Jam’iyyar APC ya kafa kwamitin musamman mai mambobi biyar domin bincikawa da kuma sasanta tsakanin mambobin jam’iyyar.

An kafa kwamitin ne domin duba batun da Shugaban jam’iyyar na ƙasa reshen Arewa maso Yamma, Salihu Moh’d Lukman, ya ɗaga a kan yadda Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu da Sakatarensa Sanata Iyiola Omisore ke gudanar da harkokin jam’iyyar.

Binciken Blueprint Manhaja ya gano kwamitin da aka kafa na ƙunshe da mambobi da suka haɗa da Abubakar Kyari a matsayin Shugaba da Emma Eneukwu da Ijeomah Arodiogbu da kumaFelix Morka.

Majiya mai tushe ta ce an cimma matsayar ɗaukar wannan matakin ne yayin taron da NWC ya gudanar a Sakatariyar jam’iyyar da ke Abuja a ranar Laraba.

A ranar Litinin Lukman ya yi ƙorafin cewa NWC ƙarƙashin jagorancin Sanata Adamu ya ci gaba da aikata kwatankwacin kurakuran da suka sabauta rushe NWC ƙarƙashin jagorancin Adams Oshiomhole a 2020.

Lukman ya yi zargin NWC ya maida sauran sassan shugabancin APC saniyar ware tun bayan kama shugabancin jam’iyyar a 2022.

Ya ce NWC ya hana sauran ɓangarorin shugabancin jam’iyyar yin aiki kamar yadda dokar jam’iyyar ta tanadar.

Daga cikin kurakuran da NWC na jam’iyyar ke tafkawa kamar yadda Lukman ya nunar, har da rashin shirya taron Majalisar Shugabannin Jam’iyya na Ƙasa (NEC), rashin shirya rahoto kan hada-hadar kuɗaɗen jam’iyyar da sauransu.

Manhaja ta gano cewa galibin mambobin NWC na tare da Lukman kan zarge-zargen da ya yi in ban da Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa da Sakatarensa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *