An sako tsohon Mataimakin Gwamnan Nasarawa bayan biyan fansar N4m

‘Yan bindiga a Jihar Nasarawa sun sako tsohon Mataimakin Gwamnan jihar da suka yi garkuwa da shi bayan da aka biya fansar Naira miliyan huɗu.

A ranar Alhamis da ta gabata ‘yan bindigar suka yi garkuwa da Farfesa Onje Gye-Wado a gidansa da ke Rinza cikin Ƙaramar Hukumar Wamba a jihar.

Da fari, masu garkuwar sun buƙaci a biya fansar Naira miliyan 70 kafin su sako shi, inda ahalinsa suka nemi ragi zuwa miliyan N3.5, wanda a ƙarshe suka biya miliyan N4 kafin aka sake shi.

Majiya ta kusa da Farfesan ta faɗa wa jaridar News Point Nigeria cewar, “Masu garkuwar sun karɓi kuɗin fansar ne a kusa da Makarantar Sankandaren Mada Hills da ke Akwanga, haɗa da katin waya na N200…”

Bayanai sun ce, bayan da aka sako shi an ɗauki Farfesa Gye-Wado zuwa Fadar Sarkin Wamba, Oriye Rindre, Mai Shari’a Lawal Musa Nagogo.