Rikicin kamfanin Seplat: kotu ta ba da umarnin Brown ya koma bakin aiki amma har yanzu an dakatar da shi a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI

Wata kotun Tarayya a jihar Legas ta janye batun umarnin da aka bayar ga shugaban zartarwa na kamfanin Seplat Energy, Roger Brown a kan ya koma bakin aikinsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, mako huɗu da suka wuce kotun ta ba da umarnin sanya takunkumi ga Brown game da ya bar cigaba da kula da al’amuran shugabancin kamfanin. Inda aka sallame shi daga muƙaminsa.

An ba wa Brown odar sauka daga muƙaminsa ne bayan masu ruwa da tsaki guda biyar daga kamfanin na Seplat sun zarge shi da wariyar launin fata da azabtar da ‘yan Nijeriya ma’aikatan kamfanin.

Kodayake, Brown da kamfanin na Seplat sun musanta wannan zargin. Amma an maye gurbinsa na wucin-gadi da shugaban aikace-aikace na kamfanin, Samson Ezugworie.

A wani jawabi na haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki da masu hannun jarin kamfanin suka bayyana a ranar Alhamis ɗin da ta gabata, ya bayyana cewa, waccan hukunci na kotu a kan Mista Brown kotun ya soke ta.

A yanzu haka dai an ɗage zaman kotun zuwa ranar 16 ga watan Mayun, 2023, don cigaba da sauraren ƙarar.

Ita dai wannan ƙara wasu mutum biyar ne waɗanda sua bayyana cewa, suna ɗaya daga cikin masu ruwa da tsaki a kamfanin suka shigar da ita.

Kodayake, har yanzu kamfanin ya kafe a kan cewa, wannan ƙarar ba ta da wani tushe ko makama. Kuma an ɗora ta ne bisa ƙarya da igiyar zato. Sannan kuma suna fatan ba da jimawa ba, kamfanin Seplat Energy zai ɗauki matakin gyara a kan lamarin.

Duk da haka, bayan dawowar Mista Brown zuwa kamfanin a matsayin shugaba, an hana shi komawa bakin aikinsa a nan Nijeriya. Saboda haka, shugaban na kamfanin man zai cigaba da gudanar da shugabancinsa a can ofishin kamfanin Seplat da ke a Ingila.

Wannan ba ya rasa nasaba da rashin warware matsala tsakanin ma’aikatar Tsare-tsare ts Nijeriya da kamfanin. Wanda ma’aikatar ta amshe lasisin aiki na Brown bayan wancan zargi da aka yi masa.

Seplat sun bayyana cewa, har yanzu suna kan tattaunawa tsakanin gwamnatin da ma’aikatar don shawo kan matsalar.