Rundunar sojin Sin ta kira taro kan yanayin tsaroa gaɓar tekun Guinea

Daga CMG HAUSA

Shugaban sashen watsa labarai na ma’aikatar tsaron ƙasar Sin kuma kakakin ma’aikatar Wu Qian, ya ce rundunar sojin ƙasar Sin ta kira taron ƙara wa juna sani ta kafar bidiyo, kan yanayin tsaron gaɓar tekun Guinea, domin tabbatar da shawarar tsaron duniya da tunanin kafa kyakkyawar makoma a kan teku, da shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar. Tare kuma da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar dake tsakanin rundunar sojin Sin da na ƙasashen dake gaɓar tekun Guinea, kan tabbatar da tsaro a kan teku.

Taken taron shi ne, “tabbatar da tsaro a gabar tekun Guinea, ta hanyar kafa kyakkyawar makoma a kan teku”.

Babban kwamishinan rundunar sojin ruwa ta ƙasar Sin, Dong Jun, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. Haka kuma, taron ya samu halartar shugabannin rundunar sojin ruwa da rundunar soji masu gadin gaɓar teku na ƙasashen dake yankin gabar tekun Guinea, da wasu shugabannin ƙungiyoyin shiyyar.

Mahalartan taron sun kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaron teku a gaɓar tekun Guinea da dauwamammen ci gaban tattalin arziki da ayyukan sojojin ruwa da matakan da ya kamata su dauka.

Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa