Rundunar sojojin Ƙasar Sin ta sha alwashin daƙile duk wani yunƙuri na tsoma hannun sassan waje cikin harkokin cikin gidan ƙasar

Daga CRI HAUSA

Kakakin ma’aikatar tsaron ƙasar Sin, Wu Qian, ya ce rundunar sojojin ƙasar za ta yi duk mai yiwuwa, wajen daƙile duk wani yunƙuri na tsoma hannun sassan waje, cikin harkokin cikin gidan ƙasar, da duk wani yunƙuri na masu burin ɓallewar yankin Taiwan, kazalika za ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da ɗinkewar sassan ƙasar Sin.

Wu Qian, wanda ya yi wannan tsokaci a Larabar nan, yayin da yake amsa tambaya game da shirin gwamnatin Amurka, na sayarwa yankin Taiwan makamai, ya ce matakin Amurkan ya yi matuƙar sabawa manufar nan ta “ƙasar Sin ɗaya tak a duniya,” da sanarwar haɗin gwiwa guda 3 da Sin da Amurkan suka amince, musamman ma wadda aka fitar bayan taron sassan biyu na ranar 17 ga watan Agusta na shekarar 1982.

Wu ya ƙara da cewa, Amurka ta aiwatar da matakai na tsoma hannu cikin harkokin cikin gidan Sin, ta kuma illata manufar ƙasar Sin game da mulkin kai da tabbatar da tsaro, kana ta haifar da koma baya, ga haɗin gwiwar sassan biyu a fannin ayyukan soji, baya ga jefa zirin Taiwan cikin yanayi na ɗar-ɗar, ta fuskar zaman lafiya da daidaito.

Jami’in ya ce Sin na fatan Amurka, za ta gaggauta soke shirin ta na sayarwa Taiwan makamai, da dakatar da duk wasu kwangiloli masu nasaba da ayyukan soji da Taiwan, ta kuma dakatar da nuna tana tare da masu burin ɓallewar yankin na Taiwan.