Gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi a Beijing za ta cimma burin qure fitar da iskar carbon mai gurvata muhalli

Daga CRI HAUSA

A matsayin gagarumar gasar wasannin motsa jiki ta ƙasa-da-ƙasa ta farko da aka shirya a ƙasar Sin, bayan da ƙasar ta tsara burikanta na kaiwa ga ƙololuwar iskar Carbon da take fitarwa, da ƙure fitar da iskar da kuma kawo ƙarshenta, kiyaye muhalli ya zama wani batu mafi jan hankalin jama’a a yayin gasar ta bana.

Ana amfani da makamashi maras gurɓata muhalli a dukkan filaye gami da ɗakunan wasannin a bana, karo na farko ke nan, da ake amfani da wutar lantarki ba tare da gurɓata muhalli ba ɗari bisa ɗari a filaye da ɗakunan wasanni na tarihin shirya gasar wasannin Olympics.

An samo yawancin wutar lantarkin da ake amfani da shi a yayin gasar ne daga wani yanki dake birnin Zhangjiakou na lardin Hebei, inda aka sauya albarkatun iska da haske a wurin, don su zama makamashin wutar lantarki ba tare da gurɓata muhalli ba, abun da ya tabbatar da gudanar da gasanni yadda ya kamata a wasu manyan yankunan gasanni uku, da suka haɗa da Beijing, da Yanqing da kuma Zhangjiakou.